: Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sallami shugaban Ma’aikatan gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Musa, daga mukaminsa nan take.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata 10/03/2026.
Sanarwar ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na sake fasalin aikin gwamnati domin inganta aiki, ƙarfafa ladabtarwa da kuma samar da kyakkyawan hidima a dukkan hukumomin gwamnati.
Gwamna Yusuf ya kuma gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan bisa gudunmawar da ya bayar da kuma jajircewarsa wajen yi wa jihar Kano hidima a lokacin da yake kan mukamin.
Ya ce, suna yi masa fatan alheri a dukkan al’amuransa na gaba, tare da addu’ar Allah Ya ba shi nasara a dukkan fannoni na rayuwarsa.”
Haka kuma gwamnan ya umarci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, wadda ke rike da mukamin babbar Sakatariya a sashen Gudanarwa da Ayyuka na Ofishin Majalisar Zartarwa (Cabinet Office), da ta riƙe muƙamin Shugabar Ma’aikatan jihar na riƙon ƙwarya har sai an naɗa wanda zai maye gurbin na dindindin.
