JIHAR JIGAWA ZA TA BI SHARI’AR SACE WALIDA ABDULHADI HAR ZUWA ƘARSHENTA – GWAMNA NAMADI
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta bi shari’ar sace ‘yar jihar, Walida Abdulhadi, har zuwa ƙarshe ta fuskar doka domin tabbatar da an yi adalci.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Laraba lokacin da ya gana da iyayen Walida tare da lauyansu a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
A yayin ganawar, gwamnan ya yi wa iyalan bayani kan halin da Walida ke ciki a halin yanzu, tare da jaddada aniyar gwamnati na tabbatar da cikakkiyar gyara, ci gaba da karatunta da kuma kula da lafiyarta gaba ɗaya.
Ya bayyana cewa a halin yanzu Walida na samun kulawar gyara a wani asibiti bisa ɗaukar nauyin Gwamnatin Jihar Jigawa. Ya ƙara da cewa da zarar an kammala shirin gyaran, za a mayar da ita hannun iyayenta domin ci gaba da rayuwa tare da su.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an tura ƙwararrun ma’aikatan jin ƙai domin ba Walida da ɗanta kulawa ta musamman da goyon bayan zamantakewa da tunani, yana mai jaddada cewa an tanadi dukkan matakan tallafi da suka dace domin tabbatar da lafiyarta da murmurewarta gaba ɗaya.
Bugu da ƙari, Gwamna Namadi ya ce gwamnatin jihar za ta mayar da Walida makaranta tare da ɗaukar nauyin karatunta baki ɗaya domin ta ci gaba da neman ilimi ba tare da wani cikas ba.
Yana mai bayyana lamarin a matsayin cikakken satar mutum, gwamnan ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da an bi dukkan hanyoyin doka domin hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin.
Haka kuma ya sanar da cewa gwamnati za ta tallafa wa Walida da iyalanta ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziƙi domin inganta rayuwarsu da taimaka musu wajen sake gina makomarsu.
A nasa jawabin, lauyan iyayen Walida, Barrista Kabiru Adamu, ya gode wa Gwamna Namadi bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen ceto yarinyar, tare da yaba wa gwamnati kan matakan da ta ɗauka na gyara da mayar da ita cikin al’umma.
Related Posts
Add A Comment
