RSANARWAR MANEMA LABARAI
GWAMNATIN JIHAR KANO TA KAKABA TSARE-TSARE MASU TSANANI GA DURBAR NA SALLAR AZUMI, DOMIN HANA TABBARBAREWAR DOKA DA TSARI
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Abba Kabir Yusuf, na sanar da al’ummar jihar da ma sauran jama’a cewa ta samu sahihan rahotannin sirri ta hannun Majalisar Tsaro ta Jiha, waɗanda ke nuna akwai yunƙurin wasu mutane na haifar da rikici da kuma tayar da hargitsi yayin bikin Sallar Azumi mai zuwa a jihar.
Duk da cewa gwamnati na da cikakken ƙuduri wajen inganta, kare da kuma adana al’adun gargajiya masu ɗimbin tarihi na Kano, tana jaddada cewa ba za ta yi sakaci da babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na tabbatar da zaman lafiya, doka da oda ba, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Dangane da haka, bayan shawarwari da Majalisar Masarautar Kano da sauran manyan masu ruwa da tsaki, gwamnati ta amince da waɗannan tsare-tsare na gudanar da bikin:
Hawan Idi (Durbar na Sallah): Za a gudanar da shi ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, daga filin Idi na Kofar Mata, ta hanyoyin da aka tanada zuwa Gidan Shettima, inda za a kammala a Kofar Fatalwa na Fadar Sarkin Kano.
Hawan Nasarawa: Za a gudanar da shi cikin wani sabon tsari amma ba a kan dawaki ba.
Hawan Daushe: An dakatar da shi a halin yanzu, kuma za a gudanar da shi a bukukuwan Sallah na gaba, Insha Allah.
Hawan Fanisau da Hawan Dorayi: Haka nan an dakatar da su na wani lokaci domin kare zaman lafiya da tsaron jama’a.
Haka kuma, an umurci dukkan hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara sintiri, su tabbatar da bin waɗannan umarni dalla-dalla, tare da ɗaukar duk matakan doka domin hana duk wani tashin hankali kafin, yayin, da bayan bikin Sallah.
Gwamnati na kira ga dukkan al’umma da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka da oda, su kuma ba jami’an tsaro haɗin kai. Haka nan tana roƙon jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana a lokacin Sallah da ma bayan haka.
Gwamnatin Jihar Kano na kuma godewa jami’an tsaro bisa jajircewa da ƙwarewarsu wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar, tare da tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da bikin Sallah cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
A ƙarshe, gwamnati na taya dukkan al’ummar Musulmi murnar zagayowar Sallar Azumi tare da fatan alheri da farin ciki.
Barka da Sallah tun da wuri.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version