TARIHIN YADUWAR ZARGIN CIN MUTUNCIN ‘YAN SIYASA A KANO DA YA KAMATA HUKUMOMI SU DAKATAR

Daga: Muhammad Suleman Gama

Manazarci kan harkokin siyasa
8 ga Agusta, 2026

Abin da ke faruwa a halin yanzu da sunan yaɗa farfagandar siyasa mara kyau da kuma cin mutuncin mutane ya wuce gona da iri, lamarin da ya kamata hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin gaggawa domin dakile shi tare da kare martabar tsarin siyasar jihar Kano.
A halin yanzu akwai dokoki da hukumomin da aka kafa domin magance irin waɗannan matsaloli. Sai dai zuwan kafafen sada zumunta na zamani, waɗanda ke bai wa kowa damar wallafa abin da yake so, ya ƙara sanya lamarin yin wahalar shawo kansa.

Akwai bambance-bambance tsakanin yadda ake yaɗa mummunar farfagandar siyasa da cin mutuncin abokan hamayya a Jamhuriyoyin Farko, na Biyu da kuma Jamhuriya ta yanzu. A yau, wasu matasa sun rungumi wasu ’yan siyasa masu tsattsauran ra’ayi, lamarin da ke sa a karkatar da su daga al’adun da al’umma ta amince da su.
DAGA ZAMANIN PRP ZUWA NPN
Idan muka waiwayi lokacin jam’iyyun PRP da NPN, musamman bayan rabuwar siyasa, za mu ga yadda wasu matasa suka bi marigayi Abubakar Rimi tare da nuna halayen siyasa masu tsauri. A gefe guda kuma, mahaifi yana goyon bayan marigayi Aminu Kano, yayin da ɗansa ke goyon bayan marigayi Rimi, duk da cewa su biyun suna fafatawa da juna a fagen siyasa.
A wancan lokaci, cin mutuncin abokan hamayyar siyasa da kuma lalata kimarsu ya kai wani matsayi mai tsanani musamman daga wasu matasa. Hakan ya sa aka fara ganin rashin girmama manya da dattawa, wanda ya saba da kyawawan ƙa’idojin al’ummar Hausawa.
Duk da haka, zamanin Rimi ya fi abin da ake gani a yanzu sauƙi, domin a lokacin akwai dattawa da shugabanni da ke taka rawa wajen gyara kurakuran matasa da kuma daidaita harkokin siyasa. A yau kuwa, rashin samun isassun dattawa da za su shiga tsakani ya ƙara sanya matsalar ta yi kamari.
Haka kuma, wasu masu ilimin addini da malamai ba su tsira daga wannan yanayi ba, lamarin da ke ƙara sanya tsarin siyasar cikin wani hali mai rauni, musamman idan aka yi la’akari da wasu shugabannin siyasa da ake zargin suna karkatar da matasa.
RAWAR KAFARON WATSA LABARAI DA SOCIAL MEDIA
Ba daidai ba ne a riƙa zargin gidajen rediyo da ke gudanar da ayyukansu bisa dokokin kafafen watsa labarai, alhali kuwa yanayin kafafen sada zumunta ya bambanta. A shafukan sada zumunta, mutum na iya zama a ɗakinsa kawai ya rubuta ko ya ɗauki wani saƙo ya watsa shi ga miliyoyin mutane a duniya ba tare da irin tsauraran matakan tantancewa da ake samu a kafafen watsa labarai na gargajiya ba.
A Kano, shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan harkokin siyasa sun fara samun karɓuwa ne tun bayan kafuwar gidajen rediyo masu zaman kansu. Waɗannan gidajen rediyo suna gudanar da ayyukansu ne bisa dokoki da ƙa’idojin da hukumomin da abin ya shafa suka gindaya.
Gidajen rediyo suna aiki ne tare da ƙwararrun editoci, yayin da Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC) ke sanya ido tare da sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukansu. Saboda haka, irin wasu abubuwan da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta a yanzu, musamman waɗanda suka shafi cin mutunci da lalata halayen mutane, ba sa samun damar watsuwa a gidajen rediyo masu bin ƙa’ida.
KANO NA BUKATAR MATKIN GAGGAWA
Kano al’umma ce mai matuƙar daraja da mutunci, don haka bai kamata a bar wannan yanayi ya ci gaba ba. Ya kamata hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumomin kula da kafafen watsa labarai da Hukumar Hisbah, su ɗauki matakan da suka dace domin dakile yaɗuwar saƙonnin siyasa masu tayar da hankali, cin mutunci da kuma lalata martabar mutane.
Bai kamata mu jira har sai an lalata mutunci da martabar al’umma saboda rashin fahimtar juna a harkokin siyasa ba.
Lokaci ya yi da hukumomin da abin ya shafa za su ɗauki mataki mai ƙarfi da gaggawa domin dawo da bin doka da oda, musamman wajen dakile yaɗuwar bayanan karya, cin mutunci da farfagandar siyasa mara kyau a kafafen sada zumunta, waɗanda ke barazana ga muhimman ƙa’idoji da dabi’un al’ummar Kano.
Daga: Muhammad Suleman Gama
Manazarci kan harkokin siyasa
8 ga Agusta, 2026

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version