WANI : MAGIDANCI MAI MATA BIYU A BAUCHI, YA KASHE DAN ACABA DON SAMUN KUDIN KARA AUREN MATA TA UKU

 

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani magidanci mai Sana’ar sayar da kayan marmari a Bauchi, saboda kashe dan acaba tare da dauke mashin dinsa don ya sayar ya samu kuɗin biyan sadakin ƙara auren mata ta uku.
Rundunar Ƴan sanda ta Jihar Bauchi ta sanar da kama mutumin mai suna Mamuda Zakaria Yau, mai shekaru 30 a duniya bisa zargin sa da caka wuƙa wa Basiru Mohammed mai shekaru 25 a duniya wanda ya ke sana’ar Achaɓa a cikin garin Bauchi.
Kamar yadda maj laifin ya shaidawa ‘Yan sanda cewa ya hau acaban daga shataletalen dogon yaro zuwa bayan tsohon airport a kan naira 600. amma da suka je wajen da babu mutane sai ya burma masa wuka a hau mashin ya kara wuta.
Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar yan ‘sandan jihar Bauchi CSP Ahmad Muhammad Wakil a nasa karin bayani cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce a ranar Alhamis 16/10/2025 da misalin karfe 9 na dare wani mai suna Mahmud Zakari Yau, mai shekaru 30 a duniya sun yi sa in sa da wani mai suna Basiru Mohammed da yake sana’ar Achaɓa wadda ya fito daga Yankin Zango Sa’idawa, a yayin sa in sar, shi Ya’u an yi zargin ya yi amfani da wuƙa ya caka wa Mohammed Dan acaba tare da yin awun gaba da babur ɗinsa kirar Bajaj launin Ja, mai lamba NNG813UM. Sai ko da aka yi sa’a Mohammed ya nemi ɗaukin mutane ta hanyar ihu, yadda maƙwabta suka kawo masa agaji tare da bin wanda ake zargin, hakan ya tilasta masa jefar da Babur ɗin, ya ranta cikin na Kare.
Bayanin ya ƙara da cewa Jami’an Yan sanda daga ofishin su dake Yelwa cikin hanzari sun isa wajen tare da ɗaukar wadda aka caka wa wuƙar zuwa Asibitin koyarwa na ATBUTH, inda likitoci suka bayyana ya rasu.
CSP Ahmad Wakil ya ƙara da cewa an ajiye gawar a Asibiti don kammala bincike da gwaje gwaje.
Kuma biyo bayan bincike an cafke wanda ake zargin ta hanyar bayanai da aka samu a cikin wayarsa da ya jefar da rigarsa mai dauke da wasu kayayyaki a cikin aljihun.
Yan sanda sun kira wasu lambobin mutane da yayi waya da su aka sanar da su cewa ya samu hatsari yana asibiti su zo. Da suka zo don kawo masa dauki aka cafke su aka je yadda yake aka kama shi.
Kuma a lokacin da ake tuhumarsa ya amsa laifinsa, inda ya alaƙanta yin kisan da cewa sharrin shaidan ne, DA kuma tsananin rashin kuɗin ƙara Mata ta uku, da hakan ya sa shi yaudarar Ɗan Achaɓan tare da caka masa wuƙa ya dauke mashin nasa don ya sayar ya samu kudin sadakin auren Mata ta uku da ya mata alkawarin aure amma abin da yake samu a sana’ar sa ta sayar da kayan marmari bata wadatar da shi yadda zai samu kudin cikawa matar alkawarin auren da ya yi mata ba.
Kakakin Rundunar yan’sanda CSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce an samu shaida a wajen da suka hada da Babur Bajaj Boxer, wuƙa mai jini a jiki,Takalmi da wayar Salula ta wadda ake zargin.
Kwamishinan yan’sanda na Jihar Bauchi CP Sani Omolori Aliyu ya bada umarni a mai da binciken zuwa Sashen binciken manyan laifuka na Rundunar wato CID don ƙara bincike tare da gabatar da mai laifin gaban Kotu.

 

YAN SANDA A BAUCHI SUN CAFKE WANDA YA KWAKULE IDON KANWAR SA DA WANDA YA SA YA KAWO MASA IDON

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Bayan afkuwar wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a wani kauye da ke kusa da garin Wailo, a ƙaramar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi, inda wani matashi mai suna Auwalu ya ƙwaƙwule idon ƙanwarsa yar shekara 7 mai suna Ruƙayya don neman biyan bukatarsa ta duniya, rundunar Yan sanda ta cika hannu da mutumin da wanda ya sa shi kawo masa idon.
Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, mahaifin yarinyar, Malam Muhammad Adamu, ya bayyana cewa wanda ake zargin ɗan uwanta ne na jini amma ya ci amanar su ta hanyar yaudarar yarinyar yadda ya aikata Mata wannan ta’annati.
Ya ce Auwalu ya ja ƙanwarsa cikin daji bisa yaudara kafin ya aikata mata wannan mummunan aiki da ya bar ta da raunuka masu tsanani a idanuwanta biyu da ya kwakule.
Bayan tonuwar da asirinsa ya yi ne aka garzaya da Ruƙayya asibitin koyarwa na ATBUTH da ke Bauchi inda likitocin ido suka yi mata aiki don gyara wajen raunukan mazaunan idanuwan biyu.
Sai ko a cewar babban likitan asibitin ido na ATBUTH, Dr. Shahir Bello Umar, ƙwararren likitan ido yace ganinta ba zai sake dawo ba lamarin da ke nufin ta makance gaba ɗaya saboda ya lalata dukkan ido biyun.
Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatarwa wa manema labarai cewa tuni jami’an tsaro suka kama wanda ake zargi da aikata laifin, harma da wanda ake zargin shi ya saka shi ya nemo idon don aikata ayyukan tsafi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi CSP Mohammed Ahmed Wakil ya tabbatar da abkuwar lamarin. Kuma kwamishinan Yan sanda na jihar Bauchi CP Omolarin Aliyu ya bayar da umarnin ci gaba da bincike don gurfanar da masu laifin a gaban kotu.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version