Jam, iyyar Apc jam, iyya ce da ta ke baiwa kowa dama ba tare da tsangwama ba A saboda haka nema Hon Tasiu Sani Dan Hajiya yake kira ga Hon DA, u Aliyu Abubakar kogunan kasar hausa ya fito neman kujerar Danmajalisar jiha, daga karamar hukumar Birnin kano.
Hon Tasiu Sani Dan Hajiya, ya yi kira ga yayan jam, iyyar Apc na karamar hukumar Birnin kano da su baiwa Hon DA, u Aliyu Abubakar kogunan kasar Hausa dama domin ya wakilci karamar hukumar Birni a majalisar Dokokin Jihar kano,a jam, iyyar Apc.
Hon Tasiu Sani Dan Hajiya ya bayyana cewar Hon Da, u Aliyu Abubakar kogunan kasar hausa ya shahara wajen taimakawa Mata da matasa da tsofaffi,
Da, u Aliyu Abubakar kogunan kasar hausa, mutum ne da yasan Darajar AL, umma da Kuma iya mu, amalla.
Hon Tasiu Sani Dan Hajiya yace kogunan kasar hausa mutum ne da ke da karamci Kuma ya shahara wajen kare kima da hakkin matasa Kuma, yana da ilimin zamani da na Islama.
lokaci yayi da matasa zasu fito da Wakilin da zai kawo cigaba Mai ma ana a yankin karamar hukumar Birnin kano.
Hon Tasiu Sani Dan Hajiya ya bayyana cewar Kogunan kasar hausa zai cigaba da baza romon Dimukradiyya a sako da lungun yankin karamar hukumar Birnin kano tare da girmama Dattawa da Mata da matasa
