Tun da farko dai ansami sa toka sa katsi tsakanin magoya bayan Sanata Barau I Jibrin da magoya bayan Hon Abba Bichi da magoya bayan Hon murtala sule Garo, yayin da wasu matasa masu goyan bayan AA Zaura da na Sanata Barau suka yi walan keluwa kana aka fafata akayi gwabso kowa yakai wa kowa hari irin na siyasa a kafafen Yada Labarai.
Kwatsam Kuma sai ga Mai magana da yawun AA Zaura Hon Dahiru Mai huddadu ya fito yana bayyana cewar a tsagaita Bude wuta irin ta siyasa, domin an samu dai – dai to, amai da baka cikin kube, kasancewar jam, iyyar dai daya ce wato APC,.
Hon Dahiru Mai huddadu ya Kara da godewa Yan gwagwarmaya na Gidan AA ZAURA bisa yadda suka fito suka kare KIMA da martabar AA Zaura a kafafen Yada Labarai, da kuma yadda suka nuna kishi. da godiya bisa kare martabar Dr Abdullahi Umar Ganduje da Hon murtala sule Garo da Hon Abba Bichi.
Babu tsoro a lamarinnmu duk da kasancewar AA Zaura bashi da wani Mukami a gwamnatin tarayya, amma Bai Gaza ba
Mai huddadu yace Nasarar Apc ake bukata da hadin Kai, kada Wanda ya Kara maida martani domin kuwa AA Zaura,
Babban burinmu A tallawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya Kai ga gaci..
Amadadin AA Zaura Hon Dahiru Ahmed Mai huddadu Ina kira ga matasan mu Yan gwagwarmaya da su tsagaita su maida wukar su cikin kube, mu sanya jam, iyyar Apc a gaba domin Nasarar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027, AA Zaura ba Mai neman rigima bane
