Adai – dai lokacin da aka samu sauyin jam, iyya tsakanin Gwamnan Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf da Tsohon jagoransa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wannan tasa wasu suka fara ganin Akwai kafar da za, a iya cin zarafin wasu daga cikin Shugabanni da ke jagorancin AL, umma a siyasance.
Wannan ce tasa Mai magana da yawun Hon AA Zaura Malam Dahiru Ahmad Mai huddadu yaja hankalin Dubban magoya bayan Hon AA Zaura dasu kauce dukkanin wasu kalamai na batanci ga Dattawan siyasar wannan zamani musanman jagora Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ko tsohon shugaban jam, iyyar Apc na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ko. Sanata Dr Ibrahim shekaru ko da makamantansu.
Hon Mai huddadu yace AA ZAURA yasha Alwashin kakkabe dukkan wasu masu batanci ga Shugabanni tare da yin Kira ga matasa Yan siyasa da su kaucewa hakan, AA Zaura ya shawarci Yan siyasa dasu tsaftace harshen su su yi ladabi da biyayya, wajen Fadar kalamai a kafafen Yada Labarai ko kafar sadarwa ta zamani.
AA Zaura yace ba duniya ba siyasar wannan zamani ta koyar da Darasi ga magoya baya, saboda haka Akwai bukatar a girmama juna da mutuntawa.
Hon Mai huddadu ya bayyana cewar AA Zaura ya bukaci Dubban magoya bayansa da su marawa Kudurin Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ciyar da Jihar kano gaba.
Hon Dahiru Ahmad Mai huddadu Yayiwa Al, ummar Jihar kano fatan Alheri tare da samun Nasara ta Kowacce fuska
