ACRSAL DA GECCI SUN YI GANGAMIN SHUKA DABINON AJUWA A MAKARANTAR ANNOOR GIDA DUBU A BAUCHI
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Domin alkinta muhalli da kare kwararowar hamada, kungiyar GECCI da ACRSAL sun gudanar da taron Gangamin shuka bishiyoyin dabinon Ajuwa a makarantar Annoor international Islamic Academy Gida dubu da ke Bauchi, domin inganta muhalli da kawo ci gaba a fannin yaki da kwararowar Hamada da bunkasa tattalin arziki.
Cikin jawabinsa Alhaji Shehu Umar wanda ya wakilci kwamishinan muhalli na jihar Bauchi Hon. Danlami Ahmed Kawule ya bayyana muhimmancin shuka itatuwa masu amfani da tarihi kamar dabino. Don haka ya bukaci Jama’a su fahimci cewa bishiyoyin dabino irin na zamani suna alkinta muhalli da kuma samar da dabino da mutane za su sayar don samun wadatar arziki. Bayan haka kuma ga inuwa da sauran amfani da ke tattare da bishiya a cikin al’umma.
Dr. Ibrahim Kabir shine shugaba da ke jagorantar shirin ACRSAL a jihar Bauchi ya bayyana cewa shuka bishiyoyin aiki ne a jihohin arewacin Nigeria 19 da Abuja wanda shirin ACRSAL ke jagoranta a karkashin ma’aikatun muhalli da noma da albarkatun ruwan.
Shirin yana samun tallafin bankin duniya da gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa.
Yace dashen dabinon Ajuwa da suka aiwatar an samu tallafin bishiyoyin guda dubu 25 daga Saudi Arabia da Algeria da Morocco kuma an raini wasu a Nigeria don haka suka bayar da irin bishiyoyin guda 50 wa makarantar ta Annoor don shukawa.
Dr. Ibrahim Kabir ya bayyana cewa sun fadada aikin zuwa makarantar FGGC Bauchi za a dasa bishiya 80 da kuma wasu 150 kuma za a tona rijiyar burtsatse don lura da yi musu ban ruwa.
Haka Kuma za a yi dashen gwadi a makarantu 15 da suka hada da ATBU da ATAP da Legal Misau da COE Azare da State University Yuli Bauchi da sauran su.
Shima shugaban hukumar yawon shakatawa ta jihar Bauchi Kuma shugaban hukumar gandun daji ta jihar Bauchi Dr. Mohammed Nasir Ibrahim ya ja hankalin shugabanni da kungiyoyi da mutanen Nigeria su himmatu wajen alkinta muhalli ta hanyar shuka bishiyoyi.
Saboda a baya iyaye da kakanni ke shuka dabino don amfanin ‘yan baya masu zuwa. Amma a yanzu an samu ci gaba Idan an shuka yau shekara kadan ake amfana wanda suka shuka ke cin moriyar.
Don haka Dr Nasir ya yaba da kokarin kungiyar GECCI DA ACRSAL game da yadda suke kokarin alkinta muhalli a jihar Bauchi da kasa baki daya.
Shima shugaban makarantar Annoor Malam Mustapha Ahmed Balarabe a nasa jawabin ya bayyana cewa za su ci gaba da renon dukkan itatuwa da aka shuka har su girma kamar yadda aka raini dukkan bishiyoyin da ke cikin makarantar kuma su ke bayar da sha’awa ga kowa. Kuma duk wanda ya sa ido a cikin makarantar Annoor international zai ga kore shar abin sha’awa.
Malam Abdulhamid Tahir Hamid shine shugaban kungiyar ta GECCI a jihar Bauchi kuma shugaban Africa na kungiyar dasa bishiyoyi don gyara muhalli.
Cikin jawabinsa yace, makasudin aikin a karkashin ma’aikatun muhalli da noma da albarkatun ruwa a kasa, shine don a hada guiwa aikin ya inganta. Kuma suna aikine a jihohi 11 wato Adamawa da Yobe da Gombe da Sokoto da Birnin Kebbi da Bauchi da Katsina da Kano da Jigawa da Borno yadda a yanzu sun raini bishiyoyin dabinon Ajuwa dubai daga irin wanda aka samo daga Saudi Arabia da Morocco da Algeria.
Yace saboda ana dasa bishiyoyi ana bari su mutu shi yasa suka karkatar da aikin zuwa cikin makarantu saboda suna da kokarin lura da bishiya kamar yadda Jamiar Bayero Kano da Maiduguri da wasu makarantu ke jagorantar wannan aiki.
Saboda a Kalla kowace bishiya ta kai naira dubu takwas kuma za a fara cin moriya cikin shekara biyar yadda cikin kankanen lokaci idan dabinon yayi kyau za a iya sayar da na naira Milyan guda cikin kankanen lokaci, kuma za a ci moriyar su tun daga yara har jikoki.
