Wasu rahotanni da jaridar kano online ta rawaito na muna cewa, majalisar kansilolin karamar hukumar Tudun Wada, ta koka akan yadda Shugabancin karamar hukumar yake aiki ba tare da saninsu ba, sai dai kawai su ji ko su gani ana yi.
Kazalika sun ce babu wata takarda ta wani aiki da ta taba shigowa gabansu, da sunan neman shawara ballantana sahalewarsu.
Kamar yadda jaridar kano online ta rawaito cewar Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, wannan koke nasu ya fito fili ne, sakamako zuwan kwamitin binciken ayyukan kananan hukumomin wanda gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya umarta ayi, karkashin jagorancin majalisar dokokin jihar Kano a yayin da ya ziyarci karamar hukumar ta Tudunwa a ranar Alhamis din da ta gabata wato 25/9/2025.
Wata majiya na nuni da cewar rashin iya aiki ne yasa ake mantawa da majalisar zartarwa ta karamar hukumar ne yasa ake yin gaban Kai.
Kansilolin sun bukaci da a maida hankali ga abinda ya shafi AL, ummar yankin ba Wai fadce – fadacen da bazasu anfani kowa ba illa Cutar da yankin.
Yanzu haka shugabar karamar hukumar na fuskantar kalubalen Shari, a bisa yunkurin tare da aikata ta, addacin siyasa ga Shugaban jam, iyyar Apc na karamar hukumar Tudun wada, tare da raunata matasa da dama
