Kamar yadda sanarwa ta gabata, daga tsohon Danmajalisar wakilai Hon Ibrahim Umar Ballah.              Hajiya zainab umar Ballah matace ga Alh Umar Usman Ballah, tsohon shugaban hukumar Daraktocin Kamfanin kasco na Jihar kano.

Hajiya zainab umar Ballah ta rasu ta bar Yaya da dama daga cikin yayan Akwai Hon Ibrahim Umar Ballah tsohon Danmajalisar wakilai na tarayya mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso, da Alh Hafiz Umar Ballah, shugaban Kamfanin jiragen Sama na AUUB Air services.

Usman Umar Ballah (JUDDU) Shima dane ga marigayiyar Wanda Jami, in hukumar kwastam ne dake Jihar kano.

Tuni dai akayi Jana, izarta, a Unguwar tudun maliki dake hanyar sheka, Kamar yadda Addinin musulinci ya tsara.

Allah ya jikan ta Allah ya yafe Mata Allah ya sanyata a Aljanna madaukakiya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version