Gwamnati ta rufe makarantar Halqatu Mu’awiyya Qur’anic Science Model da ke Sabuwar Gandu a Karamar Hukumar Kumbotso, tare da dakatar da dukkan ayyukanta na wucin gadi.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Kumbotso Malam Aminu Abdullahi ya fitar.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan da makarantar ta shirya gudanar da taron saukar Alƙur’ani ba tare da samun amincewa daga hukuma ba, a daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli, lamarin da ya sa aka dakatar da taron tare da rufe makarantar har zuwa wani lokaci.
Sanarwar ta ƙara da cewa an umurci makarantar da ta dakatar da dukkan ayyuka da taruka har sai an bi dukkan matakan da doka ta tanada tare da samun izini daga hukumomin da suka dace.
Sai dai Arewa Updates ta gano cewa, makarantar ta gayyaci Sarkin Kano na gidan Nassarawa Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ke samun goyon bayan ƴan APC, domin halartar taron saukar Alƙur’ani maimakon gayyatar Sarkin Kano na Kofar Kudu Malam Muhammadu Sanusi II wanda shi ne ke samun goyon bayan daga Gwamnatin Kano.
Ko a watan Mayu na 2025 ma Karamar Hukumar Kumbotso ta rufe wata makarantar Islamiyya a Farawa saboda gayyatar Sarkin na gidan Nassarawa saukar alkurʼani mai girma.
