An tsare Shugaban Hukumar Zabe ta Kano da wasu biyu kan zargin wanke Naira biliyan 1
Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Talata, ta bayar da umarnin tsare Sani Malumfashi, shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), tare da wasu mutane biyu a gidan gyaran hali na Kuje, bisa zargin aikata laifin wanke kudin Naira biliyan daya.
Mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da wannan umarni bayan Malumfashi da sauran wadanda ake tuhuma sun musanta laifuka shida da aka tuhume su da su, bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da su a gaban kotu.
Kotun ta umarci a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har sai an saurari tare da yanke hukunci kan bukatar belinsu ta hukuma.
Sai dai wata majiya da muka tuntuba ta bayyana cewar shugaban hukumar zaben ta jihar Kano Farfesa Sani Lawan malumfashi ya tafi Abuja.
