GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA KARA ALBASHIN SARAKUNAN GARGAJIYA DA KASHI 300 CIKIN 100.

D

Majalisar Zartarwa ta Jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ta amince da karin albashi sama da kaso 300 cikin 100 ga sarakunan gargajiya a fadin jihar, tare da sanya su cikin tsarin biyan albashi na gwamnatin jiha, yadda za su rika samun albashin kai tsaye ba tare da samu daga kananan hukumomi daga abin da suke samu daga gwamnatin tarayya ba.
Bayan zaman majalisar zartaswar a ranar litinin 25/5/2026, babban mai ba wa Gwamna shawara kan tattalin arziki, Alhaji Yahuza Adamu Ningi ya bayyana yi karin bayani cikin zantawa da manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa a gidan gwamnatin jihar Bauchi.
Yahuza Adamu Ningi, wanda ya wakilci Shugaban Ma’aikatan Jihar, Barrista Mohammed Sani Umar, ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na karfafa cibiyoyin sarakunan gargajiya domin inganta shugabanci da kuma fadada ayyukan gwamnati zuwa yankunan da ba sa samun cikakken kulawa.
Ya bayyana cewa tsawon shekaru da dama sarakunan gargajiya a jihar Bauchi na karbar alawus ne kawai ta hannun kananan hukumomi ba tare da tsari mai inganci ba, lamarin da ya rage musu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Shima kwamishinan labarai na jihar Bauchi Alhaji Usman Shehu Usman ya kara da cewa sabon tsarin zai sanya albashin Sarakunan karkashin dokokin aikin gwamnati na jiha, inda gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da dukkan matakan masarautu tun daga masu unguwanni har zuwa manyan sarakuna.
“Wannan gwamnati ta samar da tsari mai inganci da zai tabbatar da kula da dukkan cibiyoyin gargajiya daga matakin unguwanni har zuwa masarautu,” in ji shi.
Ya kara da cewa gwamnati ta umurci a tantance dukkan cibiyoyin sarakunan gargajiya a jihar, tare da nuna cewa an riga an samar wa wasu daga cikin sarakunan motocin aiki da gidaje domin kara inganta martabarsu.
Usman Shehu Usman ya bayyana cewa sabon tsarin albashin ya kasu zuwa matakai daban-daban da suka hada da sarakuna masu matakin daraja ta daya da biyu da ta uku, da kuma hakimai, inda kowanne mataki zai samu albashi bisa matsayinsa.
Sai dai ya ce yana da wahala a bayyana adadi daya saboda bambancin matsayi, amma ya jaddada cewa karin ya haura kaso 300 cikin 100 idan aka kwatanta da abin da mafi yawan sarakunan ke samu a baya.
Ya kuma ce akwai wasu daga cikin sarakunan da a baya kusan ba sa samun wani tsayayyen albashi da zai taimaka su kare martabar su tare da rike mutanen su da iyalansu.
Ya ce matakin na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da samar da sababbin masarautun hakimai da masu unguwanni domin inganta shugabanci da kuma kare martabar tarihin sarakunan gargajiya.
A cewarsa, manufar gwamnati ita ce kara daukaka martabar cibiyoyin gargajiya domin saukaka gudanar da mulki, cike guraben da gwamnati ba ta kai sosai ba, da kuma kare al’adu da tarihi.

 


Da wannan mataki, sarakunan gargajiya a jihar Bauchi za su fara aiki karkashin tsarin albashi na gwamnati kamar yadda ma’aikatan gwamnati ke gudanarwa.
Bayan haka ya ce an gyara fadar sarakunan wasu kuma an gina sabbi yayin da kuma wasu ana kan ginawa.
Kuma an BA SU sabbin motocin alfarma da motoci bus na dogarawan su da Hilux na Jamian tsaro masu rakiyar su.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version