ƘUNGIYAR AFRICAN PERINATAL SOCIETY TA YABAWA CI GABAN KIWON LAFIYA A JIGAWA, TA NEMI ƘARFAFA HAƊIN GWIWA DA GWAMNATIN JIHAR
Ƙungiyar ƙwararrun likitocin kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai ta Afirka, wato African Perinatal Society, ta yabawa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa gagarumin ci gaban da ta samu a fannin kiwon lafiya, musamman wajen kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, tare da neman ƙarin haɗin gwiwa da gwamnatin jihar domin ƙarfafa ingancin ayyukan kiwon lafiya.
An bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da tawagar shugabannin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Aliyu Labaran Dayyabu, suka kai wa Gwamna Malam Umar Namadi a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse.
Ziyarar ta bai wa tawagar damar sanar da gwamnan shirye-shiryen gudanar da Babban Taron Ƙasa da Ƙasa karo na biyu kan amfani da fasahar duban dan tayi (Ultrasound) da kuma lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, tare da neman goyon baya da haɗin gwiwar gwamnatin Jigawa gabanin taron na nahiyar Afirka.
Ana sa ran gudanar da taron daga ranar 26 zuwa 28 ga watan Agustan wannan shekara, inda manyan ƙwararrun likitoci, masu bincike, ma’aikatan lafiya da masu tsara manufofi daga sassa daban-daban na Afirka za su hallara domin tattauna hanyoyin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai ta hanyar bincike, kirkire-kirkire da haɗin gwiwar ƙwararru.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Farfesa Dayyabu ya bayyana Jihar Jigawa a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka yi fice wajen saka hannun jari a gine-ginen asibitoci da kuma bunƙasa ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Ya ce membobin ƙungiyar da suka ziyarci wasu asibitocin jihar sun gamsu da irin ci gaban da gwamnatin yanzu ta samar.
“Mun samu damar ziyartar wasu asibitoci a Jigawa kuma mun ga irin ayyukan da Mai Girma Gwamna ya yi wajen samar da ingantattun gine-gine da ɗaukar ƙwararrun ma’aikata. Wannan ne ya sa jihar ta samu nasarori wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, kuma muna alfahari da kasancewa tare da wannan ci gaba,” in ji shi.
Farfesa Dayyabu ya bayyana cewa an kafa African Perinatal Society ne a shekarar 2016 ƙarƙashin International Academy of Perinatal Medicine domin bunƙasa ilimin kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai a Afirka ta hanyar bincike, horaswa da haɗin gwiwa.
Ya ce taken taron bana ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwar ƙwararru domin inganta lafiyar mata da jarirai ta hanyar gano cutar hawan jini ga mata masu juna biyu (pre-eclampsia), hanyoyin kariya da magani, inganta amfani da fasahar Ultrasound, kula da haihuwa kafin lokaci, da amfani da fasahar sadarwa wajen kula da lafiya a yankunan karkara.
Haka kuma ya sanar da gwamnan shirinsu na kafa Cibiyar Bincike da Horaswa kan Lafiyar Mata da Jarirai ta Afirka, wadda za ta zama cibiyar musamman don horaswa, bincike na zamani da inganta ayyukan kula da lafiyar mata da jarirai.
Ya kuma roƙi gwamnatin Jigawa da ta tallafa wa taron tare da bai wa ma’aikatan lafiya daga jihar damar halarta.
A cewarsa, hakan zai bai wa likitoci, nas-nas, ungozomomi da sauran ma’aikatan lafiya damar samun ƙarin horo, gogewa ta ƙasa da ƙasa da kuma ƙwarewa a aikinsu.
Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya yi maraba da tawagar tare da yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na inganta lafiyar mata masu juna biyu da jarirai a faɗin nahiyar Afirka.
Ya bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci, yana mai cewa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙwararru da masu bincike na da matuƙar amfani wajen magance ƙalubalen kiwon lafiya.
“Ziyararku tana da muhimmanci a gare mu saboda ku ƙwararrun ma’aikatan lafiya ne da masu bincike. A matsayinmu na gwamnati, muna buƙatar haɗin gwiwa da ƙwararru da ƙungiyoyi irin taku domin inganta harkokin kiwon lafiya a Jigawa,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya ce mace-macen mata masu juna biyu da jarirai na ci gaba da zama babban ƙalubale a Najeriya, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da bincike da tsara manufofi bisa hujjoji da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙwararru domin rage matsalar.
Ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wa taron tare da ɗaukar nauyin ma’aikatan lafiya daga Ma’aikatar Lafiya da asibitocin gwamnati domin halarta.
“Muna cikakken goyon bayan manufofin wannan taro saboda mun yi imanin cewa sakamakonsa zai samar da hanyoyin da za su taimaka mana wajen ƙara inganta harkokin kiwon lafiya a Jigawa,” in ji shi.
Gwamna Namadi ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da saka hannun jari a gine-ginen asibitoci, bunƙasa ma’aikatan lafiya da aiwatar da sauye-sauye domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar baki ɗaya.
