Kamar yadda shugaban kwamitin ya bayyana Hon sale kaka kawo ya ce kimanin mutane, 150 ne yayan jam, iyyar Apc masu magana a kafafen Yada Labarai, aka baiwa wadannan kudade. Masu magana domin kare kina da martaba jam, iyyar Apc aka baiwa tallafin kudaden.
Hon sale kala kawo ya bayyana cewar, mutane 200 ne zasu Amfana da wadanda kudaden, yayin da aka baiwa mutum 150, kana nan bada dadewa ba mutane 50 zasu Amfana da wannan tallafin..

Wannan na matsayin tallafine ga yayan jam, iyyar Apc domin Kara musu karfin gwiwa duk da kasancewar Jihar kano ba Apc ce ke rike da ita ba.
Daga cikin mahlarta taron Akwai mataimakin shugaban majalisar Dattawa na kasa Sanata Barau I Jibrin Wanda ya samu wakilcin Maitaimka masa Hon shitu Madaki kunchi, Wanda yayi dogon jawabi tare da kalaman karfafa gwiwa ga mahlarta taron, kana daga bisani Yabada Naira dubu Dari 5 amadadin Sanata Barau I Jibrin.
Tsohon kwamishinan Yada Labarai Hon Muhammad Garba, ya jinjinawa kwamitin koli na yan Radio, bisa yadda suke bada gudunmawar cigaban jam, iyyar Apc a Jihar kano.
Shugaban jam, iyyar Apc na Jihar kano Hon Abdullahi Abbas Wanda sakataren jam iyyar Apc na Jihar kano ya wakilta, Hon Bashir Mai sango bukacesu da su cigaba da kare muhibbar Apc tare da yin Adawa Mai ma, ana idan akayi la akari da yadda gwamnati Mai ci ta aikata zunubi kala – kala irin na siyasa,.
Yayin da kakakin jam, iyyar Apc na Jihar kano Hon Ahmad Aruwa, ya ce wajibi ne jam, iyyar Apc ta cigaba da zama tsintsiya madauri guda domin kakkabe masu jar hula a zaben shekara ta 2027.
An karkare taron tare da wakokin jam, iyyar Apc domin Nishantar da mahalarta taron