Baya ta haihu: APC ta sauya tsarin rabon shugabancin jam’iyya a Kano zuwa 50–50 maimakon 60-40

Uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta sauya tsarin rabon iko a jihar Kano daga kaso 60–40 da ta amince da shi a farko zuwa 50–50 tsakanin bangaren Gwamna Abba Kabir Yusuf da bangaren tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.

Sauyin ya biyo bayan taron karɓar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zuwa APC a ranar 16 ga Fabrairu, wanda ya gudana a Kano

Jaridai Daily Nigerian ta rawaito cewa taron ya bar baya da Kura, inda jam’iyyar ta lura cewa, shugabannin APC na asali ne suka tara jama’a a taron ba wai Gwamnan Kano ba, hakan ne yasa ta ce da sake, wai an bai wa mai kaza kai, in da ta sake ragewa gwamna Abba kaso 10 a cikin sittin din shi, ta kara wa bangaren Ganduje da Barau.

Sabon tsarin ya tanadi rabon 50–50 tsakanin bangarorin biyu, a wani yunƙuri na tabbatar da daidaito da kuma rage rikicin cikin gida. Rahotanni sun ce shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa sun nuna rashin gamsuwa da yadda taron sauyin sheƙar bai jawo dimbin magoya bayan Kwankwasiyya ba kamar yadda ake zato.

Duk da sauyin sheƙar wasu ‘yan majalisa, kwamishinoni da shugabannin ƙananan hukumomi 44, ana ganin tushen magoya bayan Kwankwasiyya na nan daram tare da jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso.

A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, an cimma daidaito inda aka bai wa gwamnan kujeru 14 cikin 27 na shugabannin ƙananan hukumomi, yayin da bangaren Ganduje ya samu 13.

Majiyoyi sun tabbatar wa da jaridar cewa matakin ya samu amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin tabbatar da daidaito da ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar a Kano.

Masu sa ido na ganin sabon tsarin na 50–50 na iya rage zazzafan rikicin cikin gida, sai dai ana jiran a gani ko zaman lafiyar bangarorin biyu zai dore ko kuma sabbin rikice-rikice za su ɓulla a nan gaba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version