Cikin wata wasika Mai dauke dasa hannun Alh Umar Uzairu ya aikewa da Jaridar muryar Arewa Ayau., com ya bayyana dalilan da suka sa ya sake komawa Apc din

Umar Uzairu Direba  yana amfani da wannan dama domin na aiko sako gareku tare da sheda muku cewar na dawo Jam’iyyata ta APC, hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen iyayen gidana da masu ganin mutumcinmu da kuma masu ganin gudunmawar da muke iya bayarwa a Siyasar ‘Karamar Hukumar Tarauni, hakan ya biyo bayan shawarwari da tattaunawa da masana Siyasa da masu iliminta, da hujjoji bayyanannu.

Mallam Ibrahim shekarau da Mallam Salihu Sagir Takai Jagororinmu ne a Siyasance kuma iyayenmu ne a haife kuma Mallamanmu ne a ilimance, wajibi ne mu had’a kai da su mu dawo mu basu gudunmawar da muka basu a baya Dawowar Mallam Shekarau Jam’iyyar APC babbar nasara ce ga Jam’iyyar kuma yana da ala’ka da Dawowata jam’iyyar APC daman komawata Jam’iyyar ADC da nayi daman ba a son raina na tafi ba, wasu dalilai suka sanya dole na tafi kuma Alhamdulillah anshawo kan matsalar dan haka na dawo Jam’iyyata ta APC mai albarka.

Ina godiya ga duk wanda suka dinga kiraye-kirayen na Dawo APC domin ci gaba da al’amuran siyasa tare, duk abin da ya faru a baya ya faru ya wuce, ina bawa duk masoyina a jam’iyyar APC hakuri don hakika sunji rashin dadin wannan yunkurin da nayi mun yi hakuri mun dawo gidanmu za kuma mu cigaba daga inda muka tsaya in sha Allah Allah ya bamu nasara.

 

Alh Umar Uzairu Direba ya shahara wajen cigaban jam, iyyar Apc a karamar hukumar Tarauni dama Jihar kano baki daya, zuwansa na sa jam, iyyar Apc ta kara samun nasara gagaruma

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version