Taron masu ruwa da tsaki na jam, iyyar Apc na Jihar kano, yabar baya da kura, bisa la, akari da yadda, aka gudanar da taron ba, aga fuskar mataimakin shugaban majalisar Dattawa ba Sanata Barau I Jibrin (DSP) Wanda ana iya cewa shine kokoluwa a mukami a yankin Arewa, kasancewar sa na biyar a mukami, Amma Sai gashi an gudanar da taron batare da ansanya hotonsa a wajen taron ba.
Sanya hoto a cikin wajen da ake gudanar da taron yana nuni da cewar Akwai matsayi da girma na mataimakin shugaban majalisar kasa, Wanda ko da a Birnin Tarayya ana sanya hotansa dana shugaban majalisar kasa, Sai gashi a kano, anyi taron masu ruwa da tsaki babu hoton Sanata Barau babu na shugaban jam, iyyar Apc na kasa, Wanda hakan yanuna cewar Akwai lauje cikin nadi,tunda taron masu ruwa da tsaki na jam, iyyar Apc na Jihar kano akace.
A ka, Ida kamata yayi a yasanya hoton shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da da, mataimakin shugaban majalisar Dattawa, na kasa, Sanata Barau I Jibrin, dashugaban jam, iyyar Apc na kasa da shugaban jam, iyyar Apc na Jihar kano Alh Abdullahi Abbas da tsohon shugaban jam, iyyar Apc na kasa Amatsayin sa na jagoran Apc a Jihar kano,domin kaucewa bude Kofa ta Baraka domin Sai Bango ya tsage kadangare ke samun shiga.
Wani daga cikin masu taimakawa Sanata Barau I Jibrin a kafafen Yada Labarai, kwamared Adamu Abdullahi karkasara yace basuyi farin ciki da yadda aka gudanar da taron a Jihar kano, batare da an baiwa Sanata Barau I Jibrin girman da Allah ya bashi ba, wajen girmamawa da mutuntawa..
Karkasara yace, babu Abinda Sanata Barau I Jibrin ya Ke fada a kowa lokacin irin cewar kowa yazo a hada Kai adunkule a matsayin tsintsiya madaurinki daya domin Kai jam, iyyar Apc ga Nasara a zaben shekara ta 2027. domin baiwa kowa damarsa.
Babban kalubale ne a yanzu ace an fara gudanar da tarurruka a Jihar kano tare da nuna Banbanci, Wanda bazai haifi da, mai idoa ba a siyasance,
Karkasara ya Kara da cewar a wajen taron, ba, aga fuskar tsohon shugaban jam, iyyar Apc na kasa ba Dr Abdullahi Umar Ganduje da wasu jiga – jigan jam, iyyar Apc da makamantansu.
