Duk da kasancewar Iyaye Mata na fuskantar kalubale saboda rauni a fanni daban – daban na rayuwa, Sai ga wata malama da ta nuna kwazo a dai – dai lokacin da aka bar Mata makaranta Mai Dalibai da dama domin ta cigaba da shugabanci da gudanarwa amatsayin riko.
Maakarantar Ahmadu Abba Memorial Academy layin Mai taba Sani Mai nagge dake yankin karamar hukumar Gwale, yayin da wannan makaranta ta shahara wajen bada ilimi ga Dalibai Maza da Mata tun daga tushe raino zuwa matakin farko wato primary,
Yayin da shugaban Maakarantar Malam mujittapha Tijjani Alkali, ya samu damar zuwa Karin karatu a kasar marakash (marocco), Sai akaga da cewar a nemo Wanda zai cigaba da gudanar da shugabancin makarantar, bisa shawarwari da kyakykyawan nazari aka baiwa malama Amratu Usman Garba, wadda ta nuna hazaka da jajircewa, wajen ganin makarantar ta cigaba batare da wata matsala.
Malama Amratu Usman Garba tayi kokarin kula da malama da Dalibai da kuma yanayin koyo da koyarwar Kamar yadda shugaban makarantar Malam mujittapha Tijjani Alkali ya bayyana,
Shima Anasa bangaren shugaban hukumar gudanrwar makarantar Sarkin Sudan Alh Ahmad Abba musa, ya Yabawa wannan malama da malaman makarantar da Dalibai suka bada shaidar kyakykyawan aikin data yi, yayin da ake nuna a matsayin hazika jaruma jajirtacciya wajen baiwa Ilimi gudunmawar data dace.
Sarkin Sudan Alh Ahmad Abba musa Yaya ba Mata bisa kokarin data nuna da kuma kwazo data yi Yayinda daga bisani aka Bata lambar yabo da kyaututttka, bisa abin kirki data aiwatar
Fatan Yan, uwa Mata zasu cigaba da baiwa marada kunya, da cigaba da tsare gaskiya da rikon Amana
Makarantar Ahmadu Abba Memorial Academy Nursery and primary and Tahfeez makaranta ce dake baiwa Dalibai karatun boko dana Islamiyya da kuma karatun Alkur, Ani maigirma da Tajweedi.
