BARAYIN MASHIN SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Wani matashi mai suna Auwal Auta Kardi ya tsinci kansa cikin mummunan hali, bayan wasu barayin mashin sun kai masa farmaki a daren talatar da ta gabata kan hanyarsa ta komawa gida, kauyen Kardi dake cikin, Jihar Kebbi.
Bayanan da manema labarai suka samu sun nuna cewa barayin sun yi masa kwanton bauna suka abka masa tare da masa mummunan rauni daga karshe suka kwace masa mashin ɗinsa, suka guntule masa hannun hagu tare da sassara shi a kai da sauran sassan jiki kafin suka tsere.
Yanzu haka, Auwal na kwance a sashen gaggawa na Asibitin FMC Birnin Kebbi, inda yake karɓar kulawar likitoci a halin yanzu.
Lamarin ya tayar da hankulan jama’a, inda ake kira ga ’yan siyasa, ’yan kasuwa, da masu hannu da shuni da su taimaka masa wajen samun jinya da lafiyar da ta dace, musamman ganin yadda ke da karamin karfi yana neman abinci ta hanyar mashin da wani ya ba shi yake lallaba rayuwa don ciyar da iyalansa.
Da aka tuntubi rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi sun bayyana cewa rundunar na ci gaba da bincike don gano wanda suka aikata masa wannan mummunan aiki na rashin imani.
Haka kuma, al’umma sun bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa wajen dakile irin wadannan hare-hare da suka yi ƙamari a jihohin arewa, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Haka kuma an bukaci Jama’a su taimaka wa hukumomin tsaro da adduah tare da tona asirin miyagun mutane da aka san suna aikata irin wadannan ayyukan rashin imani.

