CS-SUNN ta shirya taron horaswa ga ’yan jarida kan kawar da cutar rashin jini (Anaemia) a Najeriya, a Abuja
Taron horaswa na kwanaki uku a birnin Tarayya Abuja domin Inganta rawar da kafafen yaɗa labarai za su bayar wajen Ilimintar da al’umma da kuma fafutukar kawar da cutar rashin jini (anaemia) a Najeriya. Masu ruwa da tsaki sun yi kira ga kafafen watsa labarai da su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kai, hulɗa da masu tsara manufofi, da kuma al’umma.

Taron, mai taken “Kafafen Watsa Labarai a Matsayin Ginshiƙi Don Najeriya Mai ’Yanci daga Rashin Jini”, ƙungiyar Civil Society Scaling Up Nutrition in Nigeria (CS-SUNN) ce ta shirya shi. Taron ya haɗa da ’yan jarida, ƙwararrun sadarwa da abokan hulɗa na ci gaba, domin ƙara fahimtarsu kan cutar rashin jini—yaduwarta, dalilai, illolinta da hanyoyin kariya—musamman batun faɗaɗa amfani da Multiple Micronutrient Supplements (MMS
Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Daraktan Zartarwa na CS-SUNN, Malam Sunday Okoronkwo, ya bayyana horon a matsayin mai matuƙar muhimmanci, yana mai cewa cutar rashin jini na daga cikin manyan dalilan mace-macen mata masu juna biyu a ƙasar nan, kuma tana buƙatar wayar da kai mai ɗorewa.
“Rashin jini cuta ce mai kisan gilla a ɓoye. Tana kashe rayuka ba tare da hayaniya ba, musamman a tsakanin mata masu juna biyu da yara. Magance ta na buƙatar wayar da kai sosai, rahotanni masu inganci da kuma haɗin gwiwa mai ƙarfi,” in ji Okoronkwo.
Ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin CS-SUNN da kafafen watsa labarai zai taimaka wajen sauya ra’ayoyi, motsa al’umma da kuma tilasta masu tsara manufofi ɗaukar mataki. A cewarsa, cimma burin Najeriya marar rashin jini na buƙatar shigar kafafen watsa labarai sosai, shi ya sa aka mayar da hankali kan wannan taron.
Ya ƙarfafa mahalarta da su shiga tattaunawa a buɗe, su musanya ra’ayoyi da gogewa domin tabbatar da cimma manufofin taron. Haka kuma, ya nuna damuwa kan rashin wadatar MMS a wasu jihohi, yana kira ga masu tsara manufofi da su ba da fifiko ga saye da rarraba magungunan yadda ya kamata.
A nata jawabin, Babbar Jami’ar Sadarwa ta CS-SUNN, Madam Lilian Okafor, ta ƙalubalanci ’yan jarida da su yi amfani da dukkan damar da suke da ita—lokacin shirye-shirye, kafafe da dabarun ba da labari—don wayar da kai da kuma sauya ɗabi’un jama’a game da kariyar rashin jini.
“Kafafen watsa labarai na da babban nauyi wajen magance rashin jini. Dole ’yan jarida su saka kansu a matsayin masu sauraro, su sauƙaƙa labaransu domin kowa, a kowane mataki na rayuwa, ya fahimta kuma ya ɗauki mataki,” in ji ta.
Shi ma Mr Peters Olushola, Manajan Sadarwa da Kamfen na CS-SUNN, ya ce an tsara horon ne domin gina ƙwarewar ’yan jarida wajen samar da labarai masu ƙarfi, bisa hujjoji, kan rashin jini da suka dace da manufofin ciyarwa na ƙasa.
Ya bayyana cewa zaman horon zai ƙara fahimtar mahalarta kan yaduwar rashin jini, dalilai, illoli da hanyoyin kariya a Najeriya, tare da ba da muhimmanci ta musamman ga faɗaɗa amfani da MMS a matsayin babbar dabara.
Wakiltar Daraktan Sashen Gina Jiki na Ma’aikatar Lafiya da Ci gaban Al’umma ta Tarayya, Mathew Helen Achimugu ta gabatar da takarda kan halin da ake ciki na gina jiki a Najeriya, tana mai da hankali kan ƙarancin sinadaran gina jiki da yaduwar rashin jini. Ta bayyana cewa Najeriya na fuskantar manyan ƙalubale a wannan fanni, tare da kira ga haɗin gwiwar bangarori daban-daban domin magance matsalolin.
A wani gabatarwa mai taken “Tattara Labaran Al’umma: Labaran Rayuwar Jama’a da Daidaita Labaran MMS/Rashin Jini zuwa Matakin Al’umma”, Daraktan Zartarwa na Truvine Communication, Mr Geoffrey Njoku, ya bukaci ’yan jarida da su ba da fifiko ga labaran da suka shafi rayuwar mutane kai tsaye.
Ya jaddada muhimmancin daidaita labarai da halin da al’umma ke ciki, yana mai cewa nuna ainihin abubuwan da mutane ke fuskanta zai taimaka wajen fahimtar amfanin MMS da sauran matakai wajen yaki da tamowa da rage mace-macen mata masu juna biyu.

