Cssunn ta cimma muhimman manufofi biyu da aka sanya wajen inganta zuba jari a harkar abinci mai gina jiki a Najeriya, yayinda aka samu nasarar wuce adadin da aka tsara tun da farko.

Daga rahoton sakamakon wani taron bitar aikin da CS-SUNN ta shirya , dangane da aikin da UNICEF Nigeria ta dauki nauyin gudanarwa mai taken “Increased Investment in Nutrition to Scale Up Quality Nutrition Services”, wanda ake aiwatarwa a jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) tun daga watan Oktoban 2023.

Bayanan da aka gabatar sun nuna cewa an samu sakin dala miliyan 9.57 na kasafin kudin abinci mai gina jiki gaba ɗaya. Wannan ya zarce burin da aka sanya na dala miliyan 7, wanda ke nufin an cimma kashi 135 cikin 100, wato an samu karin dala miliyan 2.57 sama da abin da aka tsara.

Haka kuma, jihohi 11 daga cikin jihohin da aikin ya shafa yanzu suna aiwatar da hutun haihuwa na tsawon watanni shida tare da cikakken albashi. A farkon aikin jihohi uku ne ke da wannan tsarin, yayin da aka sanya burin kaiwa jihohi shida. Sai dai an zarce wannan buri, inda aka kai kashi 183 cikin 100 na abin da aka tsara.

Jihohin da suka shiga tsarin sun hada da Cross River, Kebbi, Niger, Borno, Bauchi, Katsina, Yobe da Zamfara, wadanda suka hade da Lagos, Kaduna da Oyo.

A matakin kasa baki daya kuwa, yanzu akwai jihohi 21 da suka amince da tsarin hutun haihuwa na tsawon watanni shida tare da cikakken albashi.

Bugu da kari, an fitar da Naira biliyan 6.27 ta Asusun Abinci Mai Gina Jiki na Yara na jihohi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2026, inda Naira biliyan 3.77 daga cikin kudaden aka fitar a shekarar 2025 kadai.

Nasarorin da.   aka bayyana cewar bayanan, wannan ci gaba na da matukar muhimmanci saboda a Najeriya, daya daga cikin yara uku ‘yan kasa da shekaru biyar na fama da matsalar gajeruwar kafa sakamakon rashin ingantaccen abinci mai gina jiki.

Tsawaita hutun haihuwa zuwa watanni shida tare da cikakken albashi na bai wa mata damar shayar da jariransu nonon uwa zalla na tsawon watanni shida, yayin da isasshen kudin kasafin abinci mai gina jiki ke taimakawa wajen tabbatar da samar da ayyukan kula da abinci mai gina jiki ga iyalai.

An bayyana cewa wannan nasara ta samo asali ne daga hadin gwiwar gwamnatocin jihohi, ‘yan majalisu, rassan kungiyoyin farar hula (CSOs), kafafen yada labarai da abokan huldar UNICEF Nigeria.

Sai dai, CS-SUNN ta ce har yanzu akwai sauran aiki a gaba, inda za ta mayar da hankali kan tabbatar da cewa kudaden da aka saki sun koma ayyuka da hidimomi ga al’umma kai tsaye.

Haka kuma, za a yi kokarin shigar da sauran jihohi tara da ba a samu bayanan sakin kudaden ba cikin tsarin, tare da mayar da tsarin hutun haihuwa na watanni shida daga abin da yake a rubuce kawai zuwa aiwatarwa a dukkan wuraren aiki.

Kungiyar ta kuma yi kira ga jama’a da su bayyana ko jihohinsu na daga cikin jihohi 11 da suka aiwatar da tsarin, tare da yin kira ga jihohin da ba su shiga ba da su dauki matakin aiwatar da shi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version