Dattawan da Jagororin APC a Jigawa Sun Amince da Tinubu da Namadi a Matsayin ‘Yan Takarar Bai-ɗaya
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar jigawa ya fitar Malam Hamisu Muhammad Gumel, kana ya rabawa manema labarai,.

Kwamitin Dattawan da jagororin jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ya amince da tsayar da Bola Ahmed Tinubu da Umar Namadi a matsayin ‘yan takarar bai-ɗaya na shugabancin ƙasa da gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027.
An cimma wannan matsaya ne a ranar Lahadi yayin wani taron kwamitin, wanda ake ɗauka a matsayin mafi girman hukuma mai yanke shawara a jam’iyyar a jihar, tare da halartar manyan jiga-jigan APC daga sassa daban-daban.
Da yake karanta matsayar taron, shugaban APC na jihar, Hon. Ahmed Garba MK, ya bayyana cewa sun cimma wannan hukunci ne bayan dogon nazari da tattaunawa mai zurfi.
Ya ce: “Muna goyon baya kuma muna amincewa da Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin ɗan takararmu guda ɗaya na shugabancin ƙasa a 2027, haka kuma Mai Girma Gwamna, Dakta Malam Umar Namadi, a matsayin ɗan takarar gwamna guda ɗaya.”
Shugaban ya ƙara da cewa kwamitin ya ɗauki nauyin gudanar da dukkan matakan tsayar da ‘yan takarar, ciki har da sayen fom ɗin takara ga su biyun.
Ya ce: “Kwamitin tsofaffin ya amince cewa zai sayi fom ɗin takara ga shugaban ƙasa da kuma Malam Umar Namadi na jihar.”
Haka kuma, ya jaddada cewa jam’iyyar ta zaɓi hanyar haɗin kai maimakon gudanar da zaɓen fidda gwani (primaries) kafin babban zaɓe.
“Muka amince baki ɗaya mu rungumi tsarin sulhu (consensus) wajen zaɓen ‘yan takara domin zaɓen da ke tafe,” in ji shi.
Domin tabbatar da wannan tsari, kwamitin ya amince da kafa ƙungiyoyi a matakin jiha da ƙananan hukumomi domin tantance masu neman takara da tabbatar da cewa mutum guda ne zai fito a matsayin ɗan takarar bai-ɗaya a kowane matsayi—na majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin jiha.
Matsayar ta samu cikakken goyon baya daga wakilan yankunan sanata uku na jihar.
Da yake magana a madadin yankin Jigawa ta Tsakiya, Hon. Farouk Adamu Aliyu ya tabbatar da goyon bayan shugabannin jam’iyyar a jihar, yana mai cewa sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027 kuma za su sayi fom ɗinsa.
Ya kuma ƙara da cewa hakan ya shafi kujerar gwamna, inda suka amince da tsayar da Gwamna Umar Namadi a matsayin ɗan takara guda ɗaya tare da ɗaukar nauyin sayen fom ɗinsa.

 


A nasa bangaren, Alhaji Isah Muhammad Gerawa daga yankin Jigawa Arewa maso Yamma ya bayyana irin wannan matsaya, yana mai cewa sun amince da Tinubu da kuma gwamnan jihar a matsayin ‘yan takara guda ɗaya na jam’iyyar.
Shi ma Sanata Muhammad Ibrahim Kirikasamma, mai wakiltar yankin Jigawa Arewa maso Gabas, ya bayyana wannan amincewa a matsayin ta bai-ɗaya kuma da zuciya ɗaya.
Ya ce sun amince da farin ciki da gamsuwa da takarar shugaban ƙasa da kuma gwamnan jihar domin zaɓen 2027, tare da fatan alheri a gaba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version