Hon Nura Muhammad Dankadai yace kan mage ya waye babu wani Dan siyasa da yake kulawa da hagu da Dama a siyasar yankin kananan hukumomin tudun wada da DOGUWA Kamar Hon Alhassan Ado Doguwa.

Hon Nura Muhammad Dankadai yace yadda Dattawan jam, iyyar Apc na Jihar kano suka Amince da cewar Babu wani Dan takarar Gwamna da Sai Gwamna Abba haka mukeso ya zama babu wani Dan takarar Sanata a yankin kano ta kudu Sai kawu sumaila, haka bbu wani Dan takarar majalisar kasa, Sai Rt Hon Alhassan Ado Doguwa, haka zalika bbu wani Dan takarar majalisar Jiha Sai Hon sule Lawan shuwaki,

Hon Nura Muhammad Dankadai yakarkare da cewar uwa Uba ma dai babu wani dantkara a kujerar shugabancin kasa in ba Sanata Bola Ahmed Tinubu ba.

Daga cikin wadanda suka jawabi Akwai tsohon shugaban hukumar Hizba ta yankin karamar hukumar Tudun wada Malam yusuf musa Jammaje, Wanda yayi dogon bayani ga me da wadanda Hon Ado Doguwa ya samarwa aiki da kuma wadanda suka Amfana da tallafin karatu.

Malam Tijjani shehi ya bayyana Hon Alhassan Ado Doguwa da cewar shine alkiblar siyasar wannan yankin na kudancin kano.

Tsaffin shugabannin kanananan hukumomin da tsofaffin Yan majalisun Jihar kano daga karamar hukumar Tudun wada da kansiloli da masu ruwa da tsaki sun amince da tabbatar da Rt Hon Alhassan Ado Doguwa amatsayin mutum kwaya daya tilo da zai wakilci yankin karamar hukumar Tudun wada da Doguwa a majalisar wakilai ta tarayya a kakar zaben 2027.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version