Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta (OON) ya gana da masu ruwa da tsaki Akan AL, amuran da suka shafi tsaro a yankin karamar hukumar Doguwa.

Wannan ganawa ba irin ta ce ta farko ba, domin Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya dade yana baiwa harkokin tsaro mahimman ci a yankin kananan hukumomin tudun wada da Doguwa a majalisar kasa..

Kamar yadda Mai magana da yawun Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya wallafa a shafinsa, Auwal Ali Sufi utai (SLA) ya yi nuni da cewar Rt Hon Alhassan Ado ya bada motocin hawa da baburan hawa Dana adai – dai ta sahu ga dukkan, Jami, an tsaro na yankin kananan hukumomin tudun wada da DOGUWA.

Sau da yawa yakan fitar da kudade masu nauyi daga Aljihun sa domin tallafawa Jami, an tsaron yankin, da Kayayyakin aiki dan samun nutsuwa d kwanciyar hankali.

Kungiyoyin tsaro da shugabanni AL, ummar da kungiyoyin sa Kai na tsaro, na daga cikin wadanda suka halarci taron, Wanda aka gudanar a yankin karamar hukumar Doguwa.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version