Dubban mutane ne suka taru domin shaida irin Tallafin kudade da motocin hawa da kekunan Dinka da Baburan hawa da motocin Noma da zababben wakilin ƙananan hukumomin Tudun wada da Doguwa a majalisar kasa rt Hon Alhassan Ado Doguwa Sardaunan kasar hausa Mai tuta OON ya bayar ga matasa da mata na yankin mazabun Burum -Burum da Baburi da Dalawa dake karamar hukumar Tudun.

Taron angudanar da shi ne a rukunin gidaje na kwankwasiyya ajihar kano ranar Juma a 30 ga watan Oktoba 26.

Taron ya samu halartar Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf Wanda mukaddashin Gwamnan Alh murtala sule Garo ya wakilta Wanda kuma shine Babban bako da ya bayyana rt Hon Alhassan Ado Doguwa da cewar rt Hon Alhassan Ado yana sahun gaba bisa yadda ya ke rabon Romon Dimukradiyya ga Al, ummar da yake wakilta na kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa.

Hon murtala sule Garo ya ce Doguwa yana koyi da Ayyukan shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu da zababben Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf

“Bamuyi mamakin wannan Gagarumin aikin na rt Hon Alhassan Ado Doguwa ba, saboda yana cikin yan majalisun da muke Alfahari da su ajihar kano kuma suke taimakawa Al, umma a wannan jihar, muna Alfahari da shi”” inji mukaddashin Gwamnan jihar kano Alh murtala sule Garo.

Hon murtala sule Garo ya bukaci sauran yan majalisun tarayya da suyi koyi da Rt Hon Alhassan Ado Doguwa bisa yadda ya ke kaunar cigaban yankin kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa da jihar kano da Arewacin nijeriya.

Tunda farko Ajawabinsa na maraba Tsohon Kwamishina,kuma shugaban Dattawa na yankin karamar hukumar Tudun wada Alh Nura Muhammad Dankadai ya bayyana cewar rt Hon Alhassan Ado Doguwa ,ya tanadi kudade da aka baiwa mata da matasa fiye da su 300 ne suka Amfana da Tallafin Domin yin jari da Dogaro da kai baya ga motocin Noma guda goma da Baburan hawa fiye da guda 100da kekunan Dinka da Al, ummar yankin mazabun Burum -Burum da Baburi da Dalawa dake karamar hukumar Tudun wada.

.. Hon Nura Muhammad Dankadai ya ce yayi hasashen cawar jihar kano zata baiwa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu kuri, a kamar yadda Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya Alkawarta Dankadai ya ce jam, iyyar APC ce zata lashe zabubbukan da za a gudanar a jihar kano.

Daga cikin Wanda sukayi jawabi akwai Tsohon shugaban jam iyyar APC na jihar kano Alh Abdullah Abbas Wanda ya ke bayyana cewar Duk fadin jihar kano babu Tamkar rt Hon Alhassan Ado Doguwa bisa yadda zaka sa shi agaba kuma kwalliya ta biya kudin sabulu,domin kyakykyawan wakilcin sa abin misali ne, majalisar kasa ta na bukatar irin rt Hon Alhassan Ado Doguwa Domin kuwa mutum ne da ALLAH ya baiwa ikon yiwa Al, ummar Arewacin nijeriya kyakykyawan wakilcin saboda haka nema muke masa fatan samun Babbar kujera a nan gaba..

 

IMG 20261031 WA0397

A jawabinsa tsohon wakilin kano ta kudu a majalisar Dattawan kasannan kuma shugaban Dattawa na yankin karamar hukumar Doguwa sanata mas, ud El jibrin Doguwa ya bukaci dukkan mutanen yankin kano da Doguwa da Tudun wada da su tabbatar sun zabi shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu da sanata suleman Abdur Rahman kawu sumaila da Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf,domin ciyar da kano gaba ta kowacce fuska.

Daga cikin wadannan sukayi jawabai da nuna goyan baya bisa yadda rt Hon Doguwa ya bada Tallafin akwai Daya daga cikin shugabannin jam, iyyar APC na kasa Malam jamo.

Tun da farko saida rt Hon Alhassan Ado Doguwa yayi jawabi Mai tsawo yadda ya nuna girman Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf da cewar gwamna ne da ya ke kishin kano da Al, ummar jihar kano.

Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewar shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu ya jinjinawa Gwamnan Abba Kabir Yusuf bisa yadda shugaban kasa ya daga Darajar Gwamnan jihar kano agaban Gwamnonin kasan nan bisa yadda ya ke rike da Amanar Al, ummar jihar kano.

Daga cikin wadannan suka halarci taron akwai Kwamishina a hukumar kula da cigaban yankin Arewa maso yamma Tsohon wakilin ƙananan hukumomin wudil da Garko eng muhammad Ali wudil da hon Baffa Babba Dan,Agundi da Dattijo Alh Gambo Gogori da tsohon shugaban karamar hukumar kabo Hon mas, ud Yusuf Garo da Hon fa,iz Alfunduki da Hon salis Ibrahim muhammad Wakilin karamar hukumar Doguwa a majalisar Dokokin jihar kano da hon Alhassan Okoh da Hon kalid Ishaq Dubban masoya

 

Tso

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version