DOMIN INGANTA TSARO, KUNGIYAR FULANI SULLUBAWA TA GUDANAR DA TARO A BAUCHI.

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Ganin yadda kabilar Fulani ke fiskantar kalubale da dama game da zamantakewa da tattalin arziki da tsaro a Nigeria, kungiyar Fulani sullubawa reshen jihar Bauchi ta gudanar da taronta jiha don bayyana matsayin ta game da neman ingancin zaman lafiya a kowane sashe a Nigeria da kasashen Afirka.
Sarkin Sullubawan jihar Bauchi Alhaji Dr. Ibrahim Waziri masani kan harkar sadarwar zamani shine ya jagoranci gudanar da taron a dakin taro na fadar Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulaiman Adamu don hada kan Fulani sullubawa da ke zaune a sassan jihar Bauchi.
Cikin jawabinsa Dr. Ibrahim Waziri bayyana matsayin sa na dan kasa mai kishi da son zaman lafiya da hada kan Fulani don magance matsalar da suke fiskanta wacce ta shafi duk ta’adda da laifuka idan an aikata ake samun Fulani a ciki, ko Kuma a gefe guda basu san hawa ko sauka ba idan an aikata laifi ake dora musu.
Don haka ya nuna godiya ga fadar maimartaba Sarkin Bauchi saboda ba shi Sarautar Sarkin Sullubawan jihar Bauchi.
Dr Ibrahim Waziri a karon farko ya bayyana cewa ya karbi wannan sarauta ce saboda tausayin Fulani musamnan sullubawa don ganin yadda ake cin zarafin su tare da kashe su ba tare da hakkin su ba.
Saboda a halin da suke ciki tun daga kasar Sokoto da kewaye toshe kan iyakoki DA gwamnati ta yi ya haifar da matsanancin talauci da rashin aikin yi.
Hakan ya sa son zuriya ya jefa da dama cikin aikata miyagun ayyuka, daga bisani Fulani masu zaune DA dukiyar su, sun bar yankin zuwa neman tudun tsira amma duk yadda suka je ana tsangwamar su.
Ya Kara da cewa Fulani masu arziki ne da arzikin su ake fada da su ake zaluntar su. Don haka ya bukaci Fulani su kasançe masu hakuri da bin doka, saboda a Sannu kungiyar za ta bi musu hakki kan dukkan abin da ke faruwa, musamnan ya shirya kararraku kusan biyar da ya ke son shigarwa don bin hakkin ‘yan Nigeria musamnan Fulani.
Shugaban kungiyar Fulani sullubawa ta jihar Bauchi Alhaji Mohammed Abubakar da Alhaji Nasiru Garba Aminu Magayakin Bauchi da Alhaji Abubakar Usman suna cikin manyan baki da suka gabatar da jawabi a wajen taron, yadda suka ja hankalin Fulani sullubawa game da zaman lafiya tare da neman filayen zama don kiwon shanun su da kuma yin gonaki don noma abinci.
Suka ce sakacin iyaye Fulani sullubawa wajen mallakar gonaki da filin gidajen zama shi ya haifar da matsalar da ake fiskanta a halin yanzu saboda kasa ta yi daraja duk ‘yan kasuwa da yan siyasa sun karbe dazuka sun mayar gonaki.
Alhaji Abubakar Usman da Aliyu umar da Adamu Sarkin Fadar Badaromo, cikin jawabinsu na neman hada kai da kuma kokarin su na ganin an tuntubi gwamnatin jihar Bauchi don cika kudirin Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na bin hakkin Fulani don samun zaman lafiya.
Don haka a shirye suke wajen ganin kungiyar ta kafu don a samu shiga jikin gwamnatin Sanata Bala Mohammed a tabbatar da kudirin sa na farfado da labin shanu da filin kiwo da gyara burtali, kuma sun bukaci Fulani su kai yaran su makaranta.
Don haka suka bayyana aniyar su na bude ofis tare da shiga hidimar gwamnati da yan siyasa don a dama da su don su samu a shiga lamarin su a magance musu kalubale da suke fiskanta.
Alhaji Abubakar Mohammed daga yankin Dindima yace sun fi shekara 40 a yankin amma tun da wasu suka sake basu mallaki filaye ba yanzu ana neman korar su daga filayen gwamnati saboda kasa ta yi zaki.
Don haka ya ce kungiya na bukatar kudi da lokaci don kar tafiyar ta lalace su zamo an bar su kara zube basu da murya guda. DA haka ne za su samu sukunin taimakawa juna don fita daga mawuyacin hali da Fulani suka shiga a wannan lokacin.
Daga karshen taron an bayyana sunan shugabannin yankuna da kananan hukumomi, Kuma an bukaci kowane mutum da ya kai shekara 18 ya fito don yin katin jefa guri’a. Haka kuma an bukaci kowa ya rika yin rijistar yaran sa a asibiti ta hanyar zuwa awu da aihuwa a asibitocin gwamnati don Karba wa yara katin dan kasa a duk yadda ake don gudun maimaita kurkure da Fulani suka yi a baya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version