JIGAWA TA NEMI HAƊIN GWIWA DA NDDB NA ƘASAR INDIA DOMIN BUNƘASA KIYON SHANU                       DA NOMA MADARA
Gwamnatin Jihar Jigawa na duba yiwuwar kulla haɗin gwiwa da Hukumar Bunƙasa Kiwo da Samar da Madara ta Ƙasar India (NDDB) domin ƙarfafa harkar kiwon dabbobi da kuma ƙara yawan samar da madara a fadin jihar.
Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi wata babbar tawaga daga NDDB ƙarƙashin jagorancin Mista Rajesh O. Gupta, wadda ta kai masa ziyarar girmamawa a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Ziyarar ta biyo bayan wata ganawa da gwamnan ya yi da cibiyoyin kiwon madara na ƙasar India a lokacin wata ziyara ta aiki da ya kai ƙasar a bara, inda aka fara tattaunawa kan hanyoyin haɗin gwiwa domin bunƙasa fannin kiwon dabbobi a Jigawa.
Yayin da yake maraba da tawagar, Gwamna Namadi ya bayyana ziyarar a matsayin mai matuƙar muhimmanci ga bunƙasar noma a jihar, yana mai cewa tattaunawar da NDDB wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake fasalta fannin kiwon dabbobi da inganta rayuwar manoma da makiyaya.
Gwamnan ya ce ziyarar ta tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma a lokacin da ya kai ziyara ƙasar India, inda aka amince cewa tawagar NDDB za ta zo Jigawa domin zurfafa tattaunawa.
Ya kuma jaddada cewa yanayin zafin ƙasar India da na Najeriya kusan iri ɗaya ne, wanda hakan zai sauƙaƙa amfani da dabarun da India ta yi nasara da su wajen bunƙasa kiwon shanu da samar da madara.
A cewarsa, tsarin haɗin gwiwar manoma da makiyaya da India ta yi amfani da shi ya taimaka wajen mayar da ƙasar ta zama mafi girma wajen samar da madara a duniya, kuma Jigawa na da niyyar kwaikwayon irin wannan tsari.
Gwamna Namadi ya kuma bayyana cewa inganta jinsin shanu ta hanyar haɗa jinsuna (cross-breeding) da amfani da hanyoyin kimiyya kamar artificial insemination zai taimaka wajen ƙara yawan madara da shanu ke samarwa.
Ya ce a halin yanzu akwai shanu da ba sa iya samar da lita ɗaya na madara a rana, amma idan aka inganta jinsinsu, yawan madarar zai ƙaru sosai.
Har ila yau, gwamnan ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin Jigawa a shirye take ta zuba jari wajen horas da masana kimiyya da jami’an wayar da kan manoma domin tallafa wa gyaran fannin kiwon madara.

 


Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta aika da masana kimiyya da dama zuwa India domin samun ƙarin ilimi da ƙwarewa, yana mai cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na sa ran samun cikakken shirin haɗin gwiwa daga NDDB nan da ƙarshen wannan wata ko farkon watan mai zuwa domin fara aiwatar da shirin.
A nasa jawabin, shugaban tawagar NDDB, Mista Rajesh O. Gupta, ya gode wa gwamnatin Jigawa bisa damar da ta ba su na ziyartar jihar domin nazarin tsarin kiwon dabbobi da ake yi.
Ya ce ziyarar kwanaki biyu da tawagar ta yi a wasu wurare ta ba su damar fahimtar yadda ake gudanar da kiwo da kuma damar da ake da ita wajen bunƙasa fannin madara.
Ya bayyana cewa nasarar India a harkar madara ta samo asali ne daga tsare-tsaren da suka shafi dukkan sassan harkar, ciki har da kiwon dabbobi, haɗa manoma cikin ƙungiyoyi, sarrafa madara, da amfani da fasaha.
Mista Gupta ya ce a halin yanzu India ita ce ƙasa ta farko a duniya wajen samar da madara, inda take samar da kusan ton miliyan 247 na madara a duk shekara.
Tawagar NDDB ta kuma bayyana shirinta na tallafa wa Jigawa ta hanyar ba da haɗin gwiwar fasaha, horas da masana da jami’an wayar da kan manoma, da kuma kafa wasu gwaje-gwajen ayyukan kiwon madara da za su zama abin koyi domin faɗaɗa shirin a fadin jihar.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version