ECOWAS ta bayyana matuƙar damuwa kan harin da sojin Amurka suka kai a Venezuela, tana mai kira ga dukkan ɓangarori da su yi hattara tare da mutunta dokokin ƙasashen duniya da ikon ƙasa da ƙasa.
Kungiyar ta jaddada cewa tattaunawa cikin lumana ce kaɗai za ta iya samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin Venezuela, tare da goyon bayan matsayar Tarayyar Afirka da kuma kira daga wasu ƙasashen Afirka na gaggauta shiga tsakani ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya.
