GWAMNA NAMADI YA SA HANNUNSA KAN KUDIRIN KARA KASAFIN KUDIN JIGAWA, YA UMARCI A AIWATAR DA SHI yadda ya kamata
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan Kudirin Ƙarin Kasafin Kuɗi na shekarar 2026 na Jihar Jigawa da ƙananan hukumomi 27 na jihar, inda ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da an aiwatar da ƙarin kasafin kuɗin yadda ya kamata.
An gudanar da bikin sanya hannu kan kudirin ne a zauren majalisar zartarwa na Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa da ke Dutse, bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta amince da shi.
Ƙarin kasafin kuɗin ya ware Naira biliyan 46.369 ga gwamnatin jihar, yayin da aka ware Naira biliyan 17.109 ga ƙananan hukumomi 27 na jihar. Hakan ya sa jimillar ƙarin kasafin kuɗin ta kai Naira biliyan 63.478.
Wannan ƙarin kasafin kuɗi ya zo ne a daidai lokacin da kasafin kuɗin farko na shekarar 2026 na Jihar Jigawa ya kasance Naira biliyan 901.84, yayin da ƙananan hukumomi 27 suka samu jimillar kasafin kuɗi na farko da ya kai Naira biliyan 288.85.
Da yake jawabi bayan sanya hannu kan kudirin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa ƙarin kasafin kuɗin ya zama dole ne sakamakon samun wasu ƙarin kuɗaɗen shiga da suka taru ga jihar.
Ya ce an gabatar da batun ƙarin kuɗaɗen ga Majalisar Dokokin Jihar domin ta ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa ƙarin kuɗaɗen da aka samu za su bai wa gwamnatin jihar da ƙananan hukumomi damar aiwatar da wasu ƙarin ayyukan raya ƙasa.
A cewarsa, “Wannan ya nuna cewa jihar tana da damar aiwatar da wasu ƙarin ayyuka, haka nan ƙananan hukumomi ma.”
Gwamna Namadi ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa da sauran ‘yan majalisar bisa jajircewa da sadaukarwar da suka nuna wajen tabbatar da amincewa da ƙarin kasafin kuɗin.
Ya kuma yaba musu bisa gaggawar kammala tsarin dokar da ta kai ga amincewa da ƙarin kasafin kuɗin.
Haka kuma, gwamnan ya nuna godiyarsa ga kwamishinoni, ma’aikatu, hukumomi da sassa daban-daban na gwamnati, da kuma Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, bisa gudunmawar da suka bayar wajen kammala tsarin ƙarin kasafin kuɗin.
Gwamna Namadi ya kuma yi kira ga dukkan hukumomi da jami’an gwamnati da abin ya shafa da su tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin kuɗin bisa tanadin dokar da ya sanya wa hannu.
Ya ce:
“Muna godiya gare ku baki ɗaya, kuma ina kira gare ku da ku tabbatar da an aiwatar da wannan kasafin kuɗi kamar yadda aka amince da shi.”
Ya ƙara da cewa:
“Haka kuma, ina kira ga Majalisar Dokokin Jihar da ta ci gaba da gudanar da aikin sa ido, domin tabbatar da cewa wannan Dokar Kasafin Kuɗi ta amfani al’ummar Jihar Jigawa.”
Daga cikin wadanda suka halarci bikin sanya hannu akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatim; Sakataren Gwamnatin Jihar; Shugaban Ma’aikatan Gwamnati; Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati; mambobin Majalisar Zartarwar Jihar; manyan jami’ai da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar, da sauran manyan jami’an gwamnati.
