Jagoran matasan jam, iyyar APC na jihar kano Alh Muhammad fairuz,ya ce shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu masoyin Arewacin nijeriya bisa la,akari da yadda ya bujiro da dubban Ayyukan raya kasa a yankin Arewa,layin dogo da zai kai har kasar nijar da kuma karashen Iskar Gas dà samar da aikin titin kano zuwa Maiduguri da Titin kano zuwa Kaduna zuwa Abuja..

 

Game da harkar tsaro kuwa Hon Muhammad fairuz ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na iyakar kokari wajen magance matsalar.

Fairuz ya ce Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya biya yanfansho da daukar ma aikata da inganta matatun ruwa da gina Hanyoyin kwalta da bunkasa Tattalin arzikin jihar kano.

Wannan na nuni da irin yunkurinsa na bunkasa kasuwanci a JIHAR KANO.

Fairuz ya yi kira ga matasa maza da mata da su cigaba da baiwa gwamnati hadin kai da goyan baya domin kaiwa ga Nasara da akasa a gaba

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version