Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Kwamitocin Wayar da Kai

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki wani muhimmin mataki na karfafa hadin kan jam’iyya da kuma inganta mu’amala da jama’a a matakin kasa ta hanyar kaddamar da kwamitocin wayar da kai na siyasa a fadin jihar.
An bayyana wannan mataki ne a karshen wani babban taro da ya hada da masu rike da mukaman siyasa da zababbun shugabanni, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Gwamna, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha, ‘yan majalisar jiha, shugabannin kananan hukumomi, mashawarta na fasaha da na musamman, manyan mataimaka, mataimaka na musamman, da kuma shugabannin ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Gwamna Namadi ya bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce kara dankon hadin kai a jam’iyya tare da tabbatar da cewa tsarinta na aiki yana nan daram kuma a hade.
Ya ce: “Wannan kwamiti zai zagaya domin ganawa da dukkan mambobin jam’iyya a fadin jihar domin tabbatar da cewa jam’iyyar tana nan a hade.”
Dangane da wannan mataki, an tsara tsarin kwamitocin a matakin jiha, kananan hukumomi da kuma mazabu kamar haka:
Matakin Jiha:
Gwamna — Shugaba
Shugaban Jam’iyya na Jiha — Mataimakin Shugaba
Mataimakin Gwamna — Mamba
Kakakin Majalisa — Mamba
Sakataren Gwamnati — Mamba
Shugaban Ma’aikatan Gwamna — Mamba
Dukkan Sanatoci — Mamba
Kwamishinonin Ilimin Firamare, Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Lafiya, Albarkatun Ruwa, Ilimi Mai Zurfi, da Yada Labarai — Mambobi
Hon. Ibrahim Giwa — Mamba
Shugabar Mata ta Jiha — Mamba
Tsofaffin manya shida (da gwamna zai amince da su) — Mambobi
Matakin Kananan Hukumomi:
Kwamishina ko Mai Ba da Shawara — Shugaba
Shugaban Karamar Hukuma — Mataimakin Shugaba
Dan Majalisar Tarayya — Mamba
Dan Majalisar Jiha — Mamba
Dukkan Mashawarta na Musamman — Mamba
Shugaban Jam’iyya na Karamar Hukuma — Mamba
Kakakin Karamar Hukuma — Mamba
Dukkan Manyan Mataimaka — Mamba
Daraktoci da shugabannin hukumomi — Mamba
Tsofaffi uku daga karamar hukuma (mace 1, maza 2) — Mamba
Sakataren Karamar Hukuma — Mamba
Shugabar Mata ta Karamar Hukuma — Mamba
Duk shugabannin jam’iyya na jiha da shiyya a yankin — Mamba
Matakin Mazabu:
Mataimaki na Musamman ko Zababbiyar Kansila — Shugaba
Duk Mataimaka na Musamman — Mamba
Shugaban Jam’iyya na Mazabu — Mamba
Tsofaffi biyar (mata 2, maza 3) — Mamba
Sakataren Jam’iyya na Mazabu — Mamba
Shugabar Mata ta Mazabu — Mamba
Duk shugabannin jam’iyya na karamar hukuma a yankin — Mamba
Duk shugabannin jam’iyya na mazabu — Mamba
Gwamnan ya jaddada cewa duk da cewa jam’iyyar na nan daram, akwai bukatar komawa ga jama’a domin kara fahimtar su da ayyukan gwamnati.
Ya ce: “Mun san jam’iyya tana nan a hade, amma dole ne mu koma ga jama’a, mu yi musu bayani kan abin da gwamnati ke yi domin su kara yarda da ita.”
Ya kara da cewa kwamitocin za su yi aiki tukuru wajen tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki.
“Kwamitin zai gana da duk wadanda abin ya shafa, wadanda ke da korafi za a saurare su, a kuma dawo da su cikin tafiyar jam’iyya. Wadanda ba sa aiki sosai kuma za a karfafa su su zama masu himma.”
Haka kuma, ya danganta wannan shiri da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2027.
“Wannan ne ya sa muke son kwamitin ya je ya tattauna da jama’a, ya sulhunta, ya hada kan jama’a tare da wayar da su domin tunkarar zaben 2027.”
Ka’idojin aikin kwamitocin sun hada da karfafa zaman lafiya da hadin kan jam’iyya, wayar da kan jama’a, tabbatar da rajistar masu kada kuri’a da mambobin jam’iyya, gano kalubale, da kuma kyautata alaka a dukkan matakai.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version