Gwamna Namadi Ya Nada Mohammed Garba a Matsayin Sakataren JSIEC
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya amince da nadin Malam Abubakar Garba Mohammed a matsayin Sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Jigawa (JSIEC).
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu.
Yayin da yake taya sabon sakataren murna, Sakataren Gwamnatin ya bayyana cewa an yi nadin ne bisa cancanta, gaskiya da kuma kwarewa da ya nuna a aikinsa.
Malam Abubakar Garba Mohammed fitaccen mutum ne da ya shahara wajen gudanar da harkokin zabe da kuma fannin ilimi. An haife shi ranar 21 ga Fabrairu, 1960 a Karamar Hukumar Hadejia. Ya kwashe sama da shekaru talatin yana ba da gudummawa wajen bunkasa dimokuradiyya a Najeriya.
Yana da takardun karatu da dama, ciki har da digirin digirgir (Master’s) a fannin Banking da Finance daga Jami’ar Bayero da ke Kano, sannan yana da Diploma na digiri na gaba a fannin Gudanar da Zabuka daga Jami’ar Ahmadu Bello.
Ya fara aikinsa a matsayin malamin makaranta a Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha daga shekarar 1984 zuwa 1989.
Daga shekarar 1989 zuwa 2020, Garba Mohammed ya yi aiki a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a mukamai daban-daban. A karshe ya rike mukamin Darakta Janar na Gudanarwa da Siyan Kaya a ofishin INEC na Jihar Katsina.
Har ila yau, yana da kwarewa wajen kula da zabuka a kananan hukumomi da dama, kuma ya taba zama mai sa ido na kasa da kasa a babban zaben Jamhuriyar Ghana.
Wannan nadin ya fara aiki nan take.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version