Gwamna Namadi Ya Sake Jaddada Ƙudirinsa Na Kawar da Matsalar Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta Ta Hanyar Haɗin Gwiwar Sassa Daban-daban

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ɗaukar cikakkiyar hanya ta haɗin gwiwar ma’aikatu da hukumomi domin kawo ƙarshen matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da dorewa kan nasarorin da aka samu a fannin ilimi tare da ƙarfafa shirye-shiryen cikin gida da ke inganta shigar yara makaranta, ci gaba da kasancewarsu a makaranta da kuma bunƙasa iliminsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karɓi Bakuncin Daraktan Ƙasa na ƙungiyar Save the Children Nigeria, Mista Duncan Harvey, tare da tawagarsa, a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Dutse.
Gwamna Namadi ya yabawa ƙungiyar Save the Children bisa haɗin gwiwar da ta shafe fiye da shekara goma tsakaninta da Gwamnatin Jihar Jigawa, yana mai cewa ayyukan da ƙungiyar ta gudanar a fannonin ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki da kare haƙƙin yara sun taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar yara a faɗin jihar.
Ya tabbatar wa tawagar cewa duk da yake wasu daga cikin ayyukan da masu ba da tallafi ke ɗaukar nauyinsu na gab da ƙarewa, gwamnatin jihar za ta tabbatar da ci gaba da nasarorin da aka samu.
Ya ce, “Hanya mafi dacewa ta nuna godiyarmu gare su ita ce mu tabbatar da cewa mun ci gaba da kiyaye nasarorin da aka samu. Lallai za mu ci gaba da dorewa a kansu.”

Gwamnan ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen musayar ilimi, gina ƙwarewar ma’aikata da kuma ƙarfafa tsarin gudanar da ayyuka a cikin jihar.
“Za mu ci gaba daga inda kuka tsaya. Muna matuƙar godiya da duk abin da kuka yi,” in ji shi.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa ba za a iya magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar shiri guda ɗaya ba, yana mai jaddada cewa sai an samu haɗin kai tsakanin ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗaga wannan batu zuwa matakin Majalisar Zartarwa ta Jiha, inda aka bai wa kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati takamaiman nauyin dawo da yara makaranta, tare da duba ci gaban aikin a kai a kai a tarurrukan sassa da zaman Majalisar Zartarwa.

 


Gwamnan ya ce matakan da gwamnati ke ɗauka ba su tsaya kawai wajen rabon jakunkunan makaranta da kayan rubutu ba, domin wayar da kan iyaye da kuma haɗa al’umma cikin lamarin su ne ginshiƙin samun mafita mai ɗorewa.
Ya ce, “Babban ƙalubalen shi ne shawo kan iyaye da fahimtar da su muhimmancin ci gaba da tura ‘ya’yansu makaranta. Idan iyaye sun fahimci darajar ilimi, samar da kayan karatu zai zama abu mai sauƙi.”
Ya kuma bayyana cewa shirye-shirye irin su Mothers’ Forum, shirin Jigawa Lifelong Accelerated Learning (JILAL) da Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jiha (SUBEB) ke gudanarwa, shirin Ilimin Tsangaya da kuma haɗaɗɗun shirye-shiryen ilimin bai ɗaya na jihar suna taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan yaran da ke shiga makaranta da kuma tabbatar da ci gaba da zamansu a makaranta.

A cewarsa, shirin Mothers’ Forum ya yi tasiri sosai wajen sauya tunanin iyaye game da ilimi tare da ƙarfafa rawar da al’umma ke takawa wajen bunƙasa makarantu.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu jihar na da manyan makarantu na zamani guda bakwai da ke aiki, yayin da wasu manyan makarantun Tsangaya guda uku ke shirin fara ɗaukar ɗalibai.
Waɗannan makarantu na haɗa ilimin boko da na Alƙur’ani tare da samar da abinci ga ɗalibai domin ƙarfafa shiga makaranta, halartar darussa da kuma ci gaba da zama a makaranta.
Haka kuma, Gwamna Namadi ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tantance makarantun Tsangaya guda 130 masu ɗalibai sama da 70,000 domin haɗa su cikin shirye-shiryen koyon karatu da lissafi ba tare da kawo cikas ga tsarin karatun Alƙur’ani ba.
Ya ce, “Ba ma son fara wani shiri da ba za mu iya dorewa da shi ba. Saboda haka muna gina tsarin da zai kasance mai ɗorewa.

Tun da farko, Daraktan Ƙasa na Save the Children Nigeria, Mista Duncan Harvey, ya yabawa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa kyakkyawar haɗin gwiwar da aka yi tsawon shekaru goma, wadda ta ba ƙungiyar damar aiwatar da shirye-shirye masu tasiri a fannonin ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki da agajin gaggawa.
Ya ce ayyukan da aka gudanar ta hannun shirin PLANE, wanda Ofishin Harkokin Waje da Raya Ƙasashe na Birtaniya (FCDO) ke ɗaukar nauyi, da kuma shirin EYEPIN na Tarayyar Turai, sun faɗaɗa damar samun ilimi ga dubban yara masu rauni a ƙananan hukumomin Babura, Gwaram, Kafin Hausa da Malam Madori ta hanyar shirye-shiryen koyarwa na gaggawa, bunƙasa karatu da lissafi da kuma dawo da yara cikin tsarin makarantu na yau da kullum.

Harvey ya roƙi Gwamnatin Jihar Jigawa da ta ci gaba da dorewa kan nasarorin da aka samu ta hanyar tallafa wa yaran da ke komawa makarantu, tabbatar da dorewar shirye-shiryen da suka yi nasara da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa domin jawo ƙarin zuba jari a fannin ilimi

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version