GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA SOKE TAKARDUN FILAYEN KIWO DA AKA RABAWA MANOMA A DARAZO
Gwamnatin Jihar Bauchi ta soke dukkan filayen gonaki da ta raba a dazukan Aliya da Yautare da ke karamar hukumar Darazo, bayan kammala binciken kwamitin da Mataimakin Gwamna Rt. Hon. Auwal Jatau ya jagoranta don bincike kan rikicin manoma da makiyaya wanda ya jawo salwantar rayuka sa dukiya mai yawa.
Filayen kiwon biyu da ke da girman fiye da hektar 83,000 an samar da su tun cikin shekarar 1953.
Mataimakin Gwamna Alhaji Auwal Mohammed Jatau ya kara da cewa daga baya an sake tabbatar da raba wani yanki na filayen domin inganta samar da noma abinci da rage matsalar karancin filin noma da a ke fiskanta.
Cikin binciken kwamitin sun gano cewa an samu rashin daidaito wajen rarraba filayen gonakin da gwamnati ta amince a yi, wanda ya haddasa rikici da lalata amfanin gona da asarar rayuka da dukiya da raba wasu mutane da muhallin su wanda ayyukan son zuciya suka jawo.
Saboda haka, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kafa kwamitin, kuma ya bayar da umarni ga dukkan manoma da suka yi noma bana a wadannan filaye da su fice da amfanin su da zarar sun kammala girbe amfanin da suka noma, tare da alkawarin cewa gwamnatin za ta sake duba daftarin rarraba kadada 2,500 a yautare da wata 2,500 a yankin Aliya bisa tsarin bin doka da tabbatar da gaskiya.
Mataimakin Gwamnan Auwal Jatau ya tabbatar da kudirin gwamnati na wanzar da zaman lafiya bisa dalci, da kula da filayen gwamnati cikin gaskiya da kiyaye bin doka da oda.
Tun a kwanakin baya shima Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnatin sa za ta tashi tsaye wajen karbo dukkan filayen kiwo da burtaloli da aka raba wa mutane, hatta masu yin shuka zuwa bakin hanya duk za a cire a damina mai zuwa saboda hakan shine zai taimaka a samu warware matsalar rikicin manoma da makiyaya.
