JIGAWA NA GINA GINSHIƘAI MASU ƘARFI DOMIN SAUYA FASALIN NOMA — GWAMNA NAMADI
…Ya ce ana zuba jari a fannin kere-keren noma, ayyukan ƙarin ilimi ga manoma, kasuwancin noma da bincike
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shimfiɗa ginshiƙai masu ƙarfi da ɗorewa domin sauya fasalin harkar noma, ta yadda za ta zama fanni mai inganci, amfani da fasahar zamani, tare da samar da damarmaki da inganta rayuwar al’ummar jihar.
Gwamna Namadi ya bayyana hakan ne a yammacin Juma’a yayin bikin ƙaddamar da shirin Nigeria AgriConnect da kuma liyafar Shugaban Hukumar Tsarin CGIAR, wanda aka gudanar a Cibiyar Nazarin Noma ta Ƙasa da Ƙasa (IITA) da ke Ibadan.
A yayin taron, gwamnan ya yi tsokaci kan sauye-sauyen da ake samu a fannin noma a Jihar Jigawa, da kuma ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar jihar da IITA.
Ya ce dabarun bai wa noma fifiko da gwamnatinsa ta sanya a ƙarƙashin Ajandar Matakai 12 na Gina Jigawa Mai Inganci sun fara haifar da sauye-sauye na zahiri, ta hanyar zuba jari da gyare-gyaren hukumomi da nufin ƙara yawan amfanin gona, ƙarfafa sarƙoƙin darajar amfanin gona, da kuma samar da ingantaccen tsarin noma mai jure sauyin yanayi da sauran ƙalubale.
Gwamnan ya ce:
“Jigawa na daga cikin jihohin da suka fi samar da shinkafa, alkama da ridi. Muna faɗaɗa aikin ban ruwa da noman rani, muna ƙarfafa ayyukan bayar da shawarwari ga manoma, tare da faɗaɗa ayyukan kula da lafiyar dabbobi ta wayar hannu zuwa dukkan ƙananan hukumomi da mazabu 287.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kafa Hukumar Sauya Fasalin Noma (Agricultural Transformation Agency) da kuma Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo (Ministry of Livestock Development) domin samar da ingantaccen shugabanci, haɗin kai da ɗaukar alhakin gudanar da harkokin bunƙasa noma.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa zuba jarin da gwamnatinsa ke yi an tsara shi ne domin magance manyan matsalolin da ke hana bunƙasar noma, ciki har da ƙarancin damar samun kayan aikin noma na zamani, ayyukan ƙarin ilimi ga manoma, kasuwanci, bincike da kirkire-kirkire.
Ya bayyana cewa jihar ta kafa cibiyoyin kere-keren noma guda 60, waɗanda ke da tallafin taraktoci 400 da injinan girbin amfanin gona guda 60.
Haka kuma, adadin jami’an ƙarin ilimi da ke kai wa manoma shawarwari kan harkokin noma ya ƙaru zuwa kusan 2,000.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Jihar Jigawa ta shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa kan wani shirin horaswa da bunƙasa ‘yan kasuwar noma, wanda ke da burin horar da ‘yan kasuwa 10,000, tare da taimaka wajen samar da aƙalla ƙananan masana’antu da matsakaitan sana’o’i 500.
Ya ce wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sauya noma daga tsarin noman dogaro da kai kawai zuwa tsarin da ke haɗa manoma da fasaha, kuɗaɗen jari, sarrafawa, kasuwanni da sauran damarmakin kasuwanci.
Gwamna Namadi ya kuma bayyana matakan da ake ɗauka wajen sauya fasalin Cibiyar Binciken Noma ta Jihar Jigawa, inda ya ce ana sake fasalta cibiyar domin binciken noma ya fi mayar da hankali wajen magance matsalolin da manoma da sauran masu ruwa da tsaki a fannin noma ke fuskanta.
Ya ce binciken ya shafi muhimman fannoni da suka haɗa da samar da ingantattun iri, lafiyar ƙasa, ban ruwa, inganta kiwo, rage asarar amfanin gona bayan girbi, da kuma sarrafa amfanin gona.
Ya ƙara da cewa ana bayar da guraben tallafin karatu da horaswa na musamman, ciki har da shirye-shiryen Digiri na biyu (MSc) da Digirin-digirgir (PhD), domin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikatan da ake buƙata wajen dorewar sauye-sauyen da ake samu.
Gwamnan ya ce waɗannan zuba jari na tafiya ne tare da haɗin gwiwar Jihar Jigawa da IITA, wanda ke samar da wata dama ta amfani da kimiyya, bincike da fasahar zamani wajen magance ƙalubalen noma da kuma amfani da damarmakin da jihar ke da su.
Ya ce haɗin gwiwar ya mayar da hankali, da sauran fannoni, kan samar da ingantattun nau’o’in masara, waken soya da rogo, inganta lafiyar ƙasa da taswirar ƙasa, ƙarfafa tsarin samar da iri, yaƙi da kwari da cututtukan amfanin gona, gina sarƙoƙin darajar amfanin gona masu gasa a kasuwa, da kuma bunƙasa kasuwancin noma da matasa ke jagoranta.
Gwamna Namadi ya ce:
“Abin da ya fi faranta mana rai shi ne damar haɗa kimiyya da kirkire-kirkiren IITA da ƙasar Jigawa, manomanmu, hukumominmu da kuma ƙwazon matasanmu wajen kasuwanci.”
Ya jaddada cewa babban burin gwamnati shi ne tabbatar da cewa sakamakon bincike ya isa hannun manoma, fasahohin zamani su ƙara yawan amfanin gona, ƙarin samarwa ya haɗu da masana’antu da kasuwanni, sannan noma ya samar da ingantattun sana’o’i da ayyukan yi ga matasa.

Gwamnan ya ce Jihar Jigawa za ta ci gaba da aiki tare da IITA, CGIAR, Gwamnatin Tarayya, abokan hulɗar ci gaba, cibiyoyin hada-hadar kuɗi da masu zuba jari, domin mayar da ilimi da kirkire-kirkire zuwa ingantattun sakamako wajen ƙara yawan amfanin gona da inganta rayuwar manoma da sauran al’umma.

Ya bayyana cewa za a auna nasarar wannan haɗin gwiwa ne ta hanyar ƙara yawan amfanin gona, inganta lafiyar ƙasa, samar da ingantaccen tsarin iri, rage asarar amfanin gona bayan girbi, ƙarfafa sarƙoƙin darajar amfanin gona, bunƙasar kasuwancin noma, ƙara kuɗin shiga ga manoma, da kuma inganta damar samun abinci mai gina jiki.
A ƙarshe, Gwamna Namadi ya gayyaci shugabannin CGIAR System Board da sauran abokan hulɗa da su ziyarci Jihar Jigawa domin su ga da idanunsu sauye-sauyen da ke gudana a fannin noma.
Ya ce:
“Tare, bari mu nuna irin abin da zai yiwu idan kimiyya, gwamnati, manoma, matasa da kasuwanni suka haɗa ƙarfi suka yi aiki a matsayin tsari guda.”

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version