Yayin Ziyarar kwamishinan Yan’sandan Jihar jigawa ya ziyarci , Gwamna Namadi Ya Danganta Laifuka da Shan Miyagun Kwayoyi, Ya Bukaci Daukar Mataki Cikin Gaggawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa shan miyagun kwayoyi da matsalolin da suka shafi matasa na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa aikata laifuka a tsakanin matasa, inda ya bukaci a dauki matakai na hadin gwiwa da dorewa domin shawo kan wannan matsala.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Haruna Alaba Yahaya, ya kai masa a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Ziyarar ta ba kwamishinan damar gabatar da kansa a hukumance ga gwamnan tare da yi masa bayani kan tsare-tsaren da ya tanada domin inganta tsaro a fadin jihar.
Da yake jawabi a yayin ganawar, Gwamna Namadi ya lura cewa yawancin laifukan da ake samu a yanzu suna da nasaba da shan miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin matasa.
“Mun san irin laifukan da ka ambata. Yawancinsu suna da alaka da matsalolin matasa da kuma shan miyagun kwayoyi,” in ji gwamnan.
“Shan miyagun kwayoyi shi ne babban abin da ke janyo aikata laifuka. Idan muka magance wannan, za a samu raguwar laifuka sosai.”
Ya kara da cewa magance wannan kalubale na bukatar hada karfi da karfe, ta hanyar tsaurara doka da kuma amfani da hanyoyin wayar da kan al’umma, ciki har da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki.
“Za mu yi aiki tare da hukumomin da suka dace ciki har da NDLEA, sannan mu hada kai da malamai da shugabannin gargajiya domin wayar da kan jama’a. Rikice-rikicen da ke faruwa kan kananan sabani ba abin karba ba ne, dole a kawo karshensa.”
Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya, yana mai cewa tabbatar da zaman lafiya a jihar alhakin kowa ne.
“A matsayinmu na gwamnati, muna nan domin tallafa wa dukkan hukumomin tsaro… Haka kuma za mu samar da yanayi mai kyau domin ku gudanar da aikinku yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta duba matsalolin gine-gine da ke addabar wasu sassan ‘yan sanda a jihar.
Tun da fari, Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Haruna Alaba Yahaya, ya bayyana nadin nasa a matsayin babban abin girmamawa da kuma nauyi, inda ya tabbatar wa gwamnan da shirinsa na tabbatar da tsaro a fadin jihar.
“Karbar wannan mukami ya zo da cikakken umarni na tabbatar da cewa Jihar Jigawa ta kasance wuri mai tsaro ga ‘yan kasa masu bin doka, tare da zama mai tsauri ga masu aikata laifuka,” in ji shi.
Ya kuma bayyana kokarin da ake yi na inganta aikin leken asiri, kara karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma tsananta yaki da masu aikata laifuka a fadin jihar, tare da jaddada muhimmancin amincewar jama’a ga ‘yan sanda.
“Ba tare da amincewar jama’a ba, babu wata rundunar ‘yan sanda da za ta yi nasara,” in ji kwamishinan.
Hakazalika, CP Haruna ya bayyana shirin kafa wata rundunar gaggawa ta magance manyan laifuka (Violent Crime Response Unit), bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, domin kara inganta daukar mataki cikin gaggawa kan barazanar tsaro.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version