GWAMNA NAMADI: JIHAR JIGAWA ZA TA CI GABA DA ZUBA JARI A ILIMIN ‘YA’YA MATA
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce gwamnatin jiharsa za ta ci gaba da bai wa ilimin ‘ya’ya mata muhimmiyar kulawa tare da ƙara zuba jari a wannan fanni, a wani ɓangare na ƙoƙarin inganta halartar makaranta, ci gaba da zama a makaranta, kammala karatu da kuma samun kyakkyawan sakamakon ilmantarwa a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a garin Jahun, yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan tallafin karatu ga ɗalibai mata a makarantun gaba da firamare a faɗin Jihar Jigawa.
Tallafin ya haɗa da kayan makaranta guda 48,300, jakunkunan makaranta 15,000, kayan tsaftar mata (sanitary pads) 40,000, kayan rubutu guda 4,000 da littattafan motsa jiki 40,000. An samar da kayan ne domin rage nauyin kuɗaɗen karatu da ke kan iyaye tare da taimaka wa ‘ya’ya mata su ci gaba da kasancewa a makaranta.
Gwamna Namadi ya ce ilimi na daga cikin ginshiƙan hangen nesa na gwamnatinsa wajen bunƙasa jihar, yana mai cewa zuba jari a fannin ilimi wajibi ne domin gina al’umma mai ƙoshin lafiya, wadda za ta kasance mai amfani da kuma wadata.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar tana haɗa tallafa wa ɗalibai masu buƙata ta musamman da kuma inganta kayayyakin more rayuwa na makarantu, haɓaka ƙwarewar malamai, samar da kayan koyarwa da ilmantarwa, tare da ƙara buɗe wa ‘ya’ya mata hanyoyin samun ilimi. Haka kuma gwamnatin na aiwatar da sauye-sauye domin sanya ilimi ya zama mai karɓar kowa.
“Saboda haka, gwamnatina tana kallon zuba jari a fannin ilimi ba a matsayin kashe kuɗi ba, sai dai a matsayin mafi muhimmancin zuba jari wajen gina makomar Jihar Jigawa,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wannan tallafi ba wai don raba kayan makaranta kawai aka shirya shi ba, har ma domin rage matsalolin da ke hana ‘ya’ya mata halartar makaranta da ci gaba da zama a cikinta.
Ya ce tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata na da fa’ida mai yawa ga iyalai da al’ummomi, ciki har da inganta lafiyar iyali, ƙara ƙarfin tattalin arzikin gidaje da kuma bunƙasa ci gaban zamantakewa.
Gwamna Namadi ya ce gwamnatin jihar ta riga ta kammala shirye-shirye tare da bayar da kwangilolin samar da irin waɗannan kayan tallafin karatu a matakin ilimin firamare da ƙananan makarantun sakandare.
Ya ce wannan ya haɗa da kayan makaranta guda 22,500 ga makarantun ƙananan sakandare, da kuma guda 11,000 ga makarantun makiyaya, baya ga sauran kayan tallafin karatu kamar jakunkunan makaranta, takalma, akwatunan makaranta da littattafan motsa jiki.
Tallafin ya kuma shafi makarantun Tsangaya da tsarin haɗa ilimin Alƙur’ani da na zamani, inda za a samar da kayan makaranta guda 3,800 ga almajirai a makarantun Tsangaya da aka haɗa da ilimin zamani, ta hannun Hukumar Ilimin Tsangaya.
“Manufarmu ita ce haɗa tarbiyyar ɗabi’a da ilimin Alƙur’ani da koyon karatu da rubutu, ilimin lissafi, ƙwarewar rayuwa da kuma samar da hanyoyin zama ‘yan ƙasa masu amfani ga al’umma,” in ji Gwamnan.
Gwamna Namadi ya yi kira ga iyaye, malamai, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kwamitocin kula da makarantun al’umma, ƙungiyoyin farar hula da abokan hulɗar ci gaba da su bayar da cikakken goyon baya ga wannan ƙoƙari.
Ya jaddada cewa kayan tallafin karatu kaɗai ba za su tabbatar da samun ilimi mai inganci ba.
“Kayan makaranta kaɗai ba za su ilmantar da yaro ba. Jajircewar iyali, sadaukarwar malami, goyon bayan al’umma da kuma ladabin ɗalibi su ne za su mayar da waɗannan tallafi zuwa sakamako na gaskiya wajen ilmantarwa.”
A ƙarshe, Gwamna Namadi ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari wajen inganta rayuwar malamai, gina azuzuwa, samar da kayan koyarwa da ilmantarwa, ilimin ‘ya’ya mata, ilimi mai karɓar kowa da kuma sauye-sauyen tsarin ilimin Tsangaya.
Ya ce gwamnatin za ta ci gaba da yin hakan har sai kowane yaro a Jihar Jigawa ya samu damar koyon ilimi, bunƙasa da kuma bayar da gudummawa wajen ci gaban tattalin arziki da walwalar al’ummar jihar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version