Gwamnatin Kano Ta Bai Wa NDLEA Kayan Aiki Don Ƙarfafa Yaƙi Da Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta bai wa Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen kwamandan dabarun ayyuka na Kano, kayayyakin aiki domin ƙarfafa yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucinsu ba bisa ƙa’ida ba.
An miƙa kayayyakin ne a ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026, ta hannun Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomi na Jihar Kano kan Yaƙi da Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi da Fataucinsu, Lauya Muhuyi Magaji Rimin Gado, a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Da yake jawabi yayin miƙa kayayyakin, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa wannan tallafi na nuna ƙudurin gwamnatin jihar na yaƙi da laifuffukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, waɗanda ya ce suna daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa munanan ɗabi’u da matsalolin zamantakewa a cikin al’umma.
Ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta kai wani mataki mai matuƙar tayar da hankali, lamarin da ya ce yana buƙatar haɗin gwiwa da haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kanta.
A cewarsa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen samar da tallafin da ya dace ga hukumomin da ke da alhakin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucinsu ba bisa ƙa’ida ba, tare da amfani da duk hanyoyin da suka dace domin magance wannan ƙalubale da ke ƙara ƙamari.
Magaji ya jaddada cewa ingantaccen haɗin gwiwa da daidaita ayyukan hukumomin da abin ya shafa na da matuƙar muhimmanci wajen dakile wannan matsala da kuma kare makomar matasa a jihar.
A nasa jawabin bayan karɓar kayayyakin, Kwamandan Dabarun Ayyuka na NDLEA a Kano, CN Dahiru Yahaya Lawan, ya nuna godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya zo a kan kari.
Ya ce kayayyakin za su taimaka wajen ƙara ƙarfin gudanar da ayyukan hukumar, tare da inganta ƙoƙarinta na yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucinsu ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamanda Lawan ya tabbatar wa gwamnatin jihar cewa za a yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin cimma manufar da aka samar da su a kanta.
Haka kuma, ya jaddada cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, inda ya yi kira ga mazauna jihar, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ba hukumomin tsaro goyon baya domin samun nasarar magance matsalar.
Wannan tallafi na ƙara tabbatar da ƙudurin gwamnatin Jihar Kano na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma samar musu da kayan aiki domin yaƙi da laifuffukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, da nufin samar da al’umma mai zaman lafiya da tsaro, wadda ba ta fama da matsalar miyagun ƙwayoyi.
