Cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da wayar da kan jama,a na ma, aikatar yada labarai malam Balarabe kiru ya fitar.
Gwamnatin Kano Ta Fara Shirye-shiryen Bikin Cikar Najeriya Shekaru 66 Da Samun ’Yancin Kai Da Lakcar Ilmantarwa A Gidan Gwamnati
Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ta shirya lakcar ilmantarwa a zauren Coronation Hall da ke Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
An gudanar da lakcar ne ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta jihar, domin nazarin tafiyar Najeriya tun bayan samun ’yancin kai, da kuma tattauna hanyoyin gina ƙasa mai haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.
