R
Gwamnatin Zamfara Ta Zargi Bello Matawalle Da Gallaza wa ‘Yan PDP
Zamfara, Najeriya — Gwamnatin Jihar Zamfara ta tayar da kura a fagen siyasar Najeriya bayan ta zargi Ministan Tsaro na Ƙasa (Ƙarami), Bello Matawalle, da amfani da ikon gwamnatin tarayya wajen tsoratarwa, gallazawa da kuma kama ‘yan jam’iyyar PDP ba bisa ka’ida ba.
Zargin, wanda ya fito a cikin wata sanarwa ta hukuma, ya sake kunna muhawara kan amfani da hukumomin tsaro a siyasa, musamman yayin da kasar ke tunkarar shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.
A cewar gwamnatin Zamfara, wani mataimaki na musamman ga Gwamna Dauda Lawal ya shiga hannun jami’an tsaro a Abuja ba tare da sammaci, tuhuma ko umarnin kotu ba.
Gwamnatin ta ce an kwashe mutumin zuwa wurare daban-daban cikin sirri, lamarin da ta bayyana a matsayin sata da tauye haƙƙin ɗan adam, tana mai zargin cewa tasirin Ministan Tsaro Bello Matawalle ne ke bayan wannan lamari.
Sanarwar ta bayyana cewa abin takaici ne yadda hukumomin tsaro da aka kafa domin kare ‘yan kasa ke shiga harkokin siyasa, inda ake zargin ana amfani da su wajen murkushe ‘yan adawa.
“Wannan lamari barazana ce ga dimokuraɗiyya da doka,” in ji gwamnatin Zamfara.
Sakamakon haka, gwamnatin Zamfara ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta shiga tsakani domin:
Binciken zargin dalla-dalla
Kare martabar hukumomin tsaro
Dakile cin zarafin ‘yan adawa
Ta kuma gargadi cewa yin shiru kan irin wannan zargi na iya lalata amincewar jama’a ga dimokuraɗiyya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa kai tsaye daga Bello Matawalle. Babu bayani daga ofishin NSA ko hukumomin tsaro.
Masu sharhi na danganta rikicin da yawaitar sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a Zamfara, rikicin siyasa tsakanin tsohuwar gwamnati da sabuwa, kana Kuma da shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.
👉 Ku ci gaba da bibiyar shafinmu don sabbin bayanai yayin da labarin ke kara ɗaukar sabon salo.
