Gwani Malam Ahmad Abdurrahman ya ce Azumin watan Ramadan wata ne da yake da falala da Rahama acikin sa.
Malam Ahmad ya ce Allah madaukakin sarki ya fada cewar yana karbar Adduoin masu Azumi, yayin da Annabin tsira Annabi Muhammad yace ana gafartawa Dubban musulmi da suka yi aikin Alheri da tuba acikin watan na Ramadan.
Gwani Ahmad Abdurrahman ya ce Akwai tausayi ga masu karamin karfi dake Azumi, Akwai bukatar masu kudi su dinga ciyar da mabukata domin samun Babban Rabo a ranar Alkiyama.
Gwani Ahmad yayi shela ga masu hannu da shuni, da su yiwa addinin Musulunci hidima domin samun Dimbin Lada da tagomashi.
Malam Ahmad yayi bayani Mai tsawo tare da Jan hankalin matasa da su aikata Ayyukan Alheri da kyautatawa iyaye
