Hadakar Jamiyyun SDP da ADC Na El-Rufai Na Samun Koma Baya, Yayin da Shugabar Mata Ta Fice Daga SDP
An samu babban sauyi a fagen siyasar Kaduna bayan murabus ɗin Zainab Sani, shugabar mata ta jam’iyyar (SDP) a Jihar wanda hakan babban koma baya ne ga shirin haɗewar jam’iyyun SDP da ADC wanda ake dangantawa da tsohon Gwamna Malam Nasir El-Rufai.
Zainab Sani, wadda ta fito daga karamar hukumar Giwa, ta shahara wajen karfafa halartar mata a harkokin siyasa da kuma wayar da kan jama’a a fadin jihar.
ba, sai dai majiyoyi sun ce ta kammala shirin komawa jam’iyyar APC tare da mata sama da 5000 daga yankunan arewa da tsakiya na jihar matakin da ya yi daidai da yunƙurin Gwamna Uba Sani na ƙara haɗa kan al’umma a cikin tsarin mulkinsa mai fa’ida ga kowa.
Murabus ɗinta ya ƙara bayyana yadda tsarin siyasa a Kaduna ke canzawa, yayin da shugabannin ƙananan al’umma da masu tasiri ke ta rungumar tsarin mulki na Gwamna Uba Sani wanda ya dogara da tausayi, haɗin kai, da aikata ayyukan da jama’a ke gani da ido ba kawai gwaje-gwajen siyasar ‘yan kima ba.