Shugaban Yan majalisun Arewacin Nigeria zababben wakilin kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya Kai kudurin gaggawa gaban majalisar wakilai ta kasa domin ta sahale Dan sake Gina gadojin yankin yar yasa dake yankin karamar hukumar tudun wada, wadda ta shafe shekru tana ballewa duk shekara da Kuma gadar garin gada biyu dake yankin karamar hukumar Doguwa, wadda ta Kan gadar ne zaka shiga dajin falgore dake yankin karamar hukumar Doguwa. A saboda hanyace data ke amfanar da manoma da yankasuwa da makiyaya da yan boko.
Hon Doguwa yayi Kira ga majalisar kasa da gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin jihohin da sukayi makwabtka da jihar kano, domin bunkasar tattalin Arziki.
Mai magana da yawun Rt Hon Alhassan Ado Doguwa, Auwal ali sufi utai ya rawaito cewar, gadojin suna bukatar a sabunta su domin Hon Alhassan Ado Doguwa yayi yunkuri yafi sau shurin masaki wajen gyaran gadojin grin yar yasa da Kuma gadar garin gada biyu
Hon Doguwa ya bayyana cewar wadannan gadojin guda biyu suna bukatar a sabuntasu, domin kuwa an samar dasu ne tun zamanin tsohon shugaban kasa yakubu gawon aka samar da gadojin da suka hade, kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa, har zuwa kogin benue da wasu sassan kasa nijeriya
