Yayinda ya bi sahun Zababben Gwamnan Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf domin sabunta rijistar jam, iyyar Apc
Shima a yankin karamar hukumar Doguwa. Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta (OON)ya sabunta rijistar sa a Garin Dadinkowa kowa akwatin Kofar Fada
Wannan sabon shiri ne da jam’iyyarmu mai girma ta APC ta ƙaddamar na yin rijistar yayan ta ta hanyar na’ura Mai kwakwalwa, tare da Ajiye muhimman bayanai na kowanne Dan jam, iyya
Hon Alhassan Ado Doguwa , yace “na samu nasarar sabunta katin zama Dan jam, iyyar Apc a, a kwarin Kofar Fada , Mazabar Ragada, Karamar Hukumar Doguwa.
http://Doguwa
Cikin wata sanarwa Mai dauke da sa Hannun Rt Hon Alhassan Ado Doguwa, wadda mai magana da yawun sa Auwal Ali Sufi utai ya rabawa manema labarai, ta kafar sada zumunta, Domin tallafa wa wannan muhimmin shiri, na bayar da gudummawar sauƙaƙe aiki ta ₦100,000 ga kowace daga cikin mazabu 21 na zaɓe da ke cikin kananan hukumomi biyu na mazaɓarmu, domin ƙungiyoyin rijistar mazabu. Haka kuma, na bayar da ₦200,000 kowanne ga masu kula da rijista na kananan hukumomi biyu, lamarin da ya kai jimillar tallafin zuwa ₦2.5 miliyan.
Ina yabawa jami’an jam’iyyarmu da kuma magoya bayan APC bisa nasarar fara aiwatar da wannan shiri. Haka kuma, ina kira ga dukkan mambobin APC da su fito ƙwarai da gaske domin karɓa da sabunta katunan membobinsu, domin bunƙasar jam’iyyarmu da ci gaban ƙasarmu.
Allah Ya albarkaci APC, Jihar Kano, da kuma Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.
