Hon eng Muhammad Ali wudil Wanda babban kwamishina ne a hukumar kula da cigaban yankin Arewa yayi Kira ga matasa da suyi koyi da DSP Sanata Barau I Jibrin wajen neman Ilimi hakan na kunshe cikin sakon Taya murna ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa na kasa Dr Sanata Barau I Jibrin wanda ya kammala karatun Digirin, digirgir da yayi a Jami, ar Maryam Abacha.
Hon wudil ya Kara da cewar duk da kasancewar Dr Sanata Barau I Jibrin amatsayin sa na mataimakin shugaban majalisar ECOWAS, kuma mataimakin shugaban majalisar Dattawa na Nijeriya wannan Bai sa yayi kasa a gwiwa ba hasalima Kara kaimi yayi wajen neman Ilimi.
Hon Eng Muhammad Ali wudil FNSE ya taya Dr Sanata Barau I Jibrin murnar kammala wannan karatu tare da fatan zai zamo wata sabuwar Hanyar taimakawa AL, ummar kasa baki daya,.
Hon wudil ya Kara da cewar Dr Sanata Barau I Jibrin ya kawo cigaba Mai, ma, ana a yankin Arewacin kasan domin inganta Tattalin arziki.
