Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Ta Gayyaci Mawaki Tijjani Gandu Kan Zargin Karya Ka’idoji
Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Ta Gayyaci Mawaki Tijjani Gandu Kan Zargin Karya Ka’idoji

Daga Ismaila Ammai Maizare

Hukumar Tace Fina-Finai da Ayyukan Fasaha ta Jihar Kano ta gayyaci shahararren mawaki Tijjani Gandu, bisa zargin karya wasu daga cikin ka’idojin hukumar dangane da fitar da wani sabon aikin wakarsa.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ANIPR, ya fitar a madadin Sakataren Zartarwa na hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, a ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2026, hukumar ta ce ta gayyaci mawakin domin ya bayyana a gabanta.
Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin mawaka, marubuta da masu samar da wasu ayyukan adabi wajibi ne su gabatar da wakokinsu, rubuce-rubucensu ko sauran ayyukansu ga hukumar domin tantancewa da amincewa kafin su fitar da su ga jama’a.
Hukumar ta ce manufar wannan tantancewa ita ce tabbatar da cewa babu kalmomi, maganganu ko saƙonni a cikin ayyukan da za su iya tayar da zaune tsaye ko kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Ta kuma bayyana cewa dokar da ta kafa hukumar ta ba ta ikon tantancewa da kuma sanya ido kan wakoki da sauran abubuwan da suka shafi harkokin fasaha, tana mai cewa masu amfani da ‘yancin faɗin albarkacin baki su ma dole ne su kiyaye dokokin da suka shafi ayyukansu.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da aiwatar da dokokin da aka kafa ta bisa adalci, ba tare da nuna bambanci ko fifita wani mutum ko rukuni ba.
Saboda haka, hukumar ta bukaci Tijjani Gandu da ya mutunta gayyatar da aka yi masa tare da bayyana a gabanta, tana gargadin cewa rashin amsa gayyatar na iya zama rashin bin doka, wanda zai iya jawo ɗaukar ƙarin matakai kamar yadda dokokin da suka dace suka tanada.
Hukumar ta kuma yi kira ga mawaka, marubuta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar fasaha da su ci gaba da bin dokokinta domin kare zaman lafiya, doka da oda, da kuma ci gaban Jihar Kano.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version