Tun da farko dai Ibrahim Shitu Canji shine ya fara tabbatar wa da Hikima Radio batun ajiye aikin, daga bisani ƙungiyar ta sanar da ajiye aikin a hukumance.
Ƙungiyar ta ƙara sanar da raba gari da mai horas da ita Ladan Bosso.
Wata majiya tace an daɗe ana tattaunawa domin a samu daidaito tsakanin Ibrahim Canji da mai ƙungiyar wato Sanata Barau, kafin a cimma daidaiton biyan tsohon shugaban haƙƙinsa.
Kawo yanzu dai ana dakon sabuwar sanarwa daga ƙungiyar Barau FC na waɗanda za su jagorance ta.
Mai zaku ce dangane da wannan lamari??
