Mafiya yawan Matasan yankin karamar hukumar Kumbotso na cigaba da bayyana kiraye – kiraye ga tsohon Danmajalisar wakilai na tarayya Hon Ibrahim Umar Ballah, Wanda ya taimaki matasa ta Kowacce fuska, ya basu Sana, oi da Jari domin su dogara da kansu.
Wani Abun mamaki do burgewa shine yadda Hon Ibrahim Umar Ballah ya samar da Ayyukan raya kasa a dukkanin mazabun yankin karamar hukumar Kumbotso tun daga mazabar Danmaliki, zuwa Danbare, batakaye, Danbare,, kureken Sani mariri, da sauran mazabun Kowacce mazaba, Hon Ibrahim Umar Ballah yana da Ayyukan raya kasa da ya gudanar domin cigaban AL, umma.
A yanzu haka kungiyoyin Mata da matasa suna cigaba da nuna goyan baya ga Hon Ibrahim Umar Ballah Wanda ya taimakawa Matasan yankin karamar hukumar Kumbotso.
Karamar hukumar Kumbotso zata zama sabuwa ne idan har matasa suka tabbatar da kaunar su da goyan baya ga tsohon Wakilin da yasan zai iya dauko musu kitse a cikin wuta domin baiwa AL, umma romon Dimukradiyya.
Akwai Yiwuwar lashe zabe ga Ibrahim Umar Ballah,, Dukkan jam, iyyar da ya tsaya a zaben shekara ta 2027 bisa farin jinin sa ga matasa da Yan kasuwa da manya da Mata dake yankin karamar hukumar Kumbotso.
